MATSALAR TABARBAREWAR TSARO A ZAMFARA, YA ZAMA DOLE GWAMNATIN TA YI MOTSAWAR GASKIYA.... - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 9 April 2018

MATSALAR TABARBAREWAR TSARO A ZAMFARA, YA ZAMA DOLE GWAMNATIN TA YI MOTSAWAR GASKIYA....



Wannan shi ne lokaci mafi muni na rashin Tsaro da jahar Zamfara ta taba samuwar kanta.


A shekarun baya, ba jahar da ke da tarihin zaman Lafiya kamar jaharmu ta zamfara, Sai dai a 'yan shekarun nan jahar na sawun gaba wajen, rashin Tsaro. Kullum Akan Kashe mutanen da ba su ji, ba su gani ba a jahar Zamfara. 

Yayinda al'ummar karkara su ke azabtuwa da fuskantar kisan gilla Daga barayin shanu dai kullum su ke yi masu kisan dauki dai-dai tare da sace masu dukiya su kone Wadda ba su iya dauka tare da yiwa budurwai da matan Aure fyaden karfi.

Mu Kuma da ke cikin garuruwa muna fuskantar matsalolin Tsaro Daga 'yan ta'adda da sunka mayar da kisan al'umma wata Sana'a ta su, tare da lahanta mutane ba gaira ba dalili, tare da barayi da kan shiga gidajen al'umma su wawashe dukiya tare da yin gaba da kaddarorin da ke daukowa!


Hakika wannan matsalar ba ta biyunta a jahar Zamfara. Kuma kacokan wannan matsalar za mu iya dora kashi tis'in dinta ga Gwamnatin jahar Zamfara karkashin jagorancin gwamna Abdul'azizu Abubakar Yari Mafara, ganin yadda Gwamnatinsa ta ke nuna halin ko in Kula  da wannan matsalar Tun tana sabuwa.

Domin idan munka dubi abunda ya ke faruwa a kauyukkanmu na karkara, farkon wannan matsalar za a iya magance ta cikin ruwan sanyi, amma aka yi biris da su har sunka mallaki miyagun makamai. Haka zalika babban abunda ya kawo wannan matsalar a cikin garuruwanmu shi ne, tsabar rashin aikin yi ga matasa ga kuma kunnen uwar shegu da Gwamnatin ta yi da mu Matasa, ba mu da aikin yi, uwayenmu na cikin kunci na rashin biyansu hakkokansu kamar yadda ya dace a karshen wata, ga tsantsar jahilci da ya yi muna yawa, ganin yadda Gwamnatin kan ki biyan kudin Jarabawar waec da Neco kan Kari Wanda hakan kan Sanya Matasa da dama tsayawa da cigaba da karatun, daidaikun da ke da zuciyar yi, Sai sun Fara talauci ya yi masu tsaiko dole su Dena domin ba wani tallafi da Gwamnatin ke baiwa dalibbai domin karfafa su yi karatun.


Sai kuma babba matsala ita ce,  Yadda al'ummar karkara ke kokawa da cewa ko da sun tseguntawa hukuma Labarin masu aikata aika-aikar kwana biyu bayan an Kama su ta'addar ake Sako su, tare da sanar da su 'yan ta'addar Wanda ya tona masu asiri. Daga karshe sai ka tarar an yiwa shi Wanda ya baiwa jami'an Tsaron Labarin aukuwar abun assha! An Kashe shi, kashin gilla tare da tozarci. Wanda hakan ne, silar da ya sa ba kasafai ake samun hadin kan 'yan kauyen ba. Wanda hakan na nuna akwai jami'an Tsaron da, da su ake hada Kai wajen Kara jefa jahar Zamfara cikin kuncin rashin Tsaro.

Dan haka muddun ana son yin maganin wannan matsalar, Sai ita Gwamnatin jahar Zamfara, ta Sanya a ranta cewa tana bukatar kawo karshen wannan matsalar, ta hanyar shawo kan matsalolin da sunka zama silar tarwatswar al'amurran. 

Ya zama dole Gwamnatin jahar Zamfara ta tashi tsaye wajen Kare rayukkan jama'a da dukiyoyinsu. Domin wallahi wannan masifar ta yi muni matukar gaske!

Haka dole a sanyawa jami'an tsaronmu Ido domin bata-garin cikinsu ne, ke Kara assasa wannan masifar.


Daga karshe muna rokon Allah ya sa wannan koken namu ya kai ga kunnuwan wadanda munka yi domin su, ya kuma  ba su ikon kawo muna dauki. Allah kana amsar addu'o'in bayinka a Duk lokacin da sunka roke ka. Ya Allah muna rokonka ka kawo muna karshen wadannan tashe-tashen hankullan, ka kawo muna dawwamammen zaman Lafiya a jaharmu ta zamfara, yankin Arewa dama Najeriya baki daya. Allahumma amin.


Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Muryar Talaka Ta Kasa Reshen Jahar Zamfara) 08069807496

9-4-2018

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here