ZUWA GA SUFETO JANAR NA 'YAN SANDAR NAJERIYA, WA YAKE WAWURE KUDIN 'KANANAN 'YAN SANDA (POLICE), NA WATANNI BIYU? - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Wednesday, 4 April 2018

ZUWA GA SUFETO JANAR NA 'YAN SANDAR NAJERIYA, WA YAKE WAWURE KUDIN 'KANANAN 'YAN SANDA (POLICE), NA WATANNI BIYU?


Wannan shi ne wata na biyu da, da dama daga cikin jami'an Tsaron Najeriya na 'yan sanda (police) su ka ganin ana wawure masu kudade na ba gaira ba dalili.

A zantawar da Muryar Talaka Reshen jahar Zamfara ta yi da wasu jami'an Tsaron da sunka kawo wa kungiyar koke har ofishinta, sun koka kwarai da ganin yadda ake WAWURE masu kudi ba gaira ba dalili.

Jami'an 'yan SANDAR sun shedawa kungiyar cewa; "wannan shi ne wata na biyu, da ake wawure karanci Naira dubu talatin-talatin (30,000) a cikin albashinmu.

"Wasu daga cikin manyan ma har Naira Naira dubu tamanin da biyar (85,000) ake wawure masu.

"Mun yi kokarin  zuwa shalkwatarmu don mu yi wa kwamishina bayani, an ce mu Dan jira.

"Kamar yadda kunka sani jami'in Tsaro baya yin zanga-zanga. Shi sa ya munka kawo maku koke, dan Muryarmu ba ta fita."

Hakika wannan babbar matsala ce Wadda ya kamata SUFETO JANAR NA YAN SANDAR NAJERIYA (IG IDRIS K. IBRAHIM) ya Sanya bakinsa tare da tabbatar da cewa an gano inda matsalar take tare da kokarin ganin cewa an magance ta.

Domin wallahi hakan na iya ingiza daga cikin bata garin cikinsu zuwa ga aikata assha.


Daga karshe muna rokon Allah ya sa kokenmu ya Kai ga kunnuwan wadanda munka yi domin su.


Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau Pro I Muryar Talaka Reshen jahar Zamfara.

4-4-2018

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here