Daga, Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau
A yau Litinin 1-4-2018 kungiyar Labour Room Global Initiative, ta ga gudanar da gangamin tsaftace muhalli a babban Birnin jahar ZAMFARA wato Gusau.
Gangamin Wanda ya Fara daga Makarantar Sikandire ta Sambo Sikandire, da ke tudun wada Gusau. 'ya'yan Kungiyar sun cigaba da tsaftace magudanun ruwa, Shara, da kuma kawar da abubuwan ki a muhalin jama'a. Tare da rarraba Kasidu masu dauke da fadakarwa Akan muhimmancin tsaftace Kai da muhalli, musamman ganin damina na tafe.
A cewa Shugaba Shugaban kungiyar na jahar Zamfara, Ambasada Nura Isah Gusau, kungiyar ta shirya wannan gangamin ne, Dan fadakarwa ga al'umma akan muhimmancin tsaftace Kai da muhalli tare da marawa yunkurin Gwamnati na tsaftace muhalli. A cewarsa, ba zai yuyuwa al'umma su ce komi Sai Gwamnati ta yi masu ba.
Gangamin Wanda ya samu halartar Matasa da dama daga lungu da Sako na jahar Zamfara. Tare biyar muhimmai daga cikin lungunan garin Gusau, tare da tukewa a shataletalen Bello Bara'u da ke Gusau.


