KUNGIYAR DALIBBAN JAHAR ZAMFARA TA YI TUR DA ALLAH WADDAI DA KASHE-KASHEN AL'UMMAR DA KE FARUWA A JAHAR. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 31 March 2018

KUNGIYAR DALIBBAN JAHAR ZAMFARA TA YI TUR DA ALLAH WADDAI DA KASHE-KASHEN AL'UMMAR DA KE FARUWA A JAHAR.


Muna amfani da wannan damar wajen jajantawa 'yan uwa da abokan arzikin na Bawar Daji da ke karamar Hukumar Anka, Akan kisan gillar da barayin shanu sunka yi masu

Hakika ba mu da wasu tarin kalmomi da za mu yi amfani da su wajen sanyayawa ko rage maku wannan radadin da ya same ku, Sai dai da ya ke Allah maji rokon bayinsa NE, muna amfani da wannan damar wajen rokon Allah ya jikan wadanda sunka rasa rayukkansu, ya baiwa wadanda sunka ji raunukka, Lafiya. Su kuma iyalai da al'ummar da aka yiwa wannan kisan gillar Allah ya ba su ikon jure wannan rashin.

A 'yan kwanakin da sunka wuce ma an Yiwa mutun 40 kisan gilla a kauyen Birane, Kwatsam! Yanzu kuma sama da 100 sun bakunci kushewarsu. Hakika kungiyar Dalibban jahar Zamfara (NUZAMSS) ta damu Matuka da irin wadannan KASHE-KASHEN rashin imanin da ake yiwa al'ummar da ba su ji ba su ga gani ba a jahar....

Dan haka Kungiyar Dalibban jahar Zamfara (National Union of Zamfara State Students) na kira ga Gwamnati, Jami'an Tsaro da su dauki matakin Kare rayukkan Matasa da al'ummar jahar Zamfara Kwata. Haka zalika ya zama wajibi ga Gwamnatin Zamfara ta dauki matakin damko wadannan 'yan ta'adda domin su fuskanci koliya

Haka zalika muna kira ga al'ummar jahar Zamfara da mu natsu, mu cigaba da Goyawa Gwamnatin jaharmu  baya tare da rokon Allah ya ba su ikon hukunta wadannan 'yan ta'addan

A madadin Dukkanin dalibban jahar (NUZAMSS) muna amfani da wannan dama domin mika sakon jajantawa ga 'yan uwa da abukkan arzikin wadannan bayin Allah, Allah ya ba su ikon jure wannan rashin. Su kuma wadanda sunka riga mu gidan Gaskiya, Allah ya jikansu da RAHAMA, ya sa aljanna firdausi ce a makomarsu, ya baiwa wadanda sunka jikkata Lafiya

*Allah taimake mu baki daya*
* Allah taimaki NUZAMSS*
* Allah ya taimaki JAHAR ZAMFARA*
*Allah ya taimaki Kasarmu NAJERIYA.*

*Daga ofishin watsa Labarai na Kungiyar dalibban Zamfara (NUZAMSS)* A Madadin Shugaban Kungiyar

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here