CIGABA DA KASHE-KASHEN AL'UMMA A JAHAR ZAMFARA, DAUKAR MATAKIN GWAMNATIN ZAMFARA DA TA TARAYYA YA ZAMA WAJIBI! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Friday, 30 March 2018

CIGABA DA KASHE-KASHEN AL'UMMA A JAHAR ZAMFARA, DAUKAR MATAKIN GWAMNATIN ZAMFARA DA TA TARAYYA YA ZAMA WAJIBI!

Hakika cigaba da KASHE-KASHEN al'ummar jahar ZAMFARA din ake cigaba da yi, ya yi muni matukar gaske, la'akkari da kusan kullum Daren Allah ta'alla Sai an Kashe rai ko an raunata al'ummar da ba su ji ba su gani.
Al'ummar karkara a jahar ZAMFARA kullum cikin tashin hankali su ke, yau a yi garkuwa da su gobe a yiwa 'ya'yansu mata da matayensu na Aure fyaden karfi.
Hakika Duk wanda ya shigo kauyukkan jahar Zamfara, ya ga yadda barayin ke yawo da miyagun makamai ba tare da fargabar komi ba, zai yi matukar mamaki. Tare tambayar anya akwai Gwamnati a Zamfara? 
Mai girma gwamna, Abdul'Azizu Abubakar Yari, mun tabbatar da cewa wannan matsalar ta fi karfin gwamnatinka koma miye. Dan haka muna kira gareka da ka dauki matakin fadakar da Gwamnatin tarayya wannan matsalar da jaharka ke fuskata ta hanyar neman tallafin jami'an Tsaron da za su iya murkushe wadannan azzaluman barayin da ke kokarin maida jahar ZAMFARA kufai.
Daga haka mu ke rokon Allah ya tona asirin masu hannu a wannan aika-aikar, ya hana masu jin dadin duniya da lahira, ya kawo sauki, dauki da salama ga mu al'ummar jahar Zamfara da ake kashewa kullum.
Allah muna rokonka ka kawo muna zaman Lafiya Mai Dorewa, Allahumma amin.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.  (Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Muryar Talaka Ta Kasa Reshen Jahar Zamfara). 08069807496

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here