A yau ne, majalissar dokokin jahar zamfara ta kawo karshen zagayen jin ra'ayin jama'a a Duk fadin jahar. Akan wasu kudurori shida da ake son yiwa gyaran fuska.
Babban gudurin da ya fi Jan hankalin kungiyar Muryar Talaka shi ne; kudurin baiwa kananan hukumomi 'yancin karbar kudaden Kai tsaye daga Gwamnatin tarayya.
Kai Tsaye dai ita Gwamnatin jahar ZAMFARA ba ta son a baiwa kananan hukumomin jahar 'yancinsu.
Sai dai Alhamdulillahi kungiyar Muryar Talaka na cikin kungiyoyi biyu da sunka yi magana a wajen Taron. Wato Muryar Talaka da kuma kungiyar ma'aikatan kananan Hukumomin jahar Zamfara.
Dukkaninmu mun nuna goyon bayanmu ga baiwa kananan hukumomin Najeriya 'yancin karbar kudadensu da kuma wasu hakkoki nasu. Kuma ra'ayin talakawan jahar ZAMFARA kenan. Domin baiwa kananan hukumomin 'yancin zai taimaka matukar gaske wajen rage radadin talauci, Samar da ayukkan yi, da kuma yiwa al'ummar da ke kasa ayukkan bunkasar rayuwarsu.
Dan haka za mu zura Ido mu gani, shin ita majalissar dokokin za ta dauki ra'ayin mu mu talakawan da munka zabe su, Dan su Kare muradunmu, ko za su bi ra'ayin kansu, ta hanyar dadawa Gwamnatin jahar ZAMFARA!
Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau Pro 1 Muryar Talaka Reshen Jahar Zamfara.
30-3-2018

