CIKAKKEN LABARIN YADDA AKA KASHE MUTANE A KAUYEN BAWAR DAJI NA JAHAR ZAMFARA. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Thursday, 29 March 2018

CIKAKKEN LABARIN YADDA AKA KASHE MUTANE A KAUYEN BAWAR DAJI NA JAHAR ZAMFARA.


Mun samu zantawa, ta wayar salula da Mani (Ya nemi a sakaya sunansa). Wanda ya kirani daga cikin Gundumar Dan Gulbi da ke karamar Hukumar Maru,Jahar Zamfara. Inda su ke cigaba da gudun hijira bayan 'Yan ta'adda sun yiwa al'ummar kauyensu na Bawar Daji da ke karamar Hukumar ANKA kisan gilla a jiya laraba 28-3-2018 da shekaranjiya.


"Hakika wadannan barayin sun matsa muna. Da farko sun saci wata mata Sai da aka ba su Naira Naira dubu Dari biyu sunka Sako ta, haka zalika sunka dawo sunka Kama matar wani Sai da ya biya Naira miliya daya. Sunka zo, sunka dauki wani yaro, mu al'ummar garin, munka cewa wallahi bai yuyuwa, Sai sunka dawo da YARON.

"Sai sunka ce Sai mun gani, Dan mun San farmaki za su kawo muna Dan haka munka fita kariyar kanmu a bakin garin, bayan mun za ci ba za su zo ba, Sai sunka zo, sunka Kashe mutun sha biyar (15) an zo wajen ja'izarsu, sunka dawo sunka Kashe Duk masu Jana'izar baki daya mutun biyu kawai na tsira da rayuwarsu, yanzu haka kusan mutun hamsin (50) sunka Kashe, domin wasu gawarwaki na cikin jeji yanzu haka".


Barayin shanu dai sun dade suna cin karensu babu babbaka a kauyukkan jahar Jahar, Duk dai kasa, da makonni biyu kenan da Kashe Shugaban barayin Wanda ake Kira Buharin Daji.


Post Bottom Ad

Responsive Ads Here