KUNGIYAR MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA TA GANA DA GWAMNAN GWAMNONI A YAU
Yau Laraba 21-3-2018 kungiyar Muryar Talaka Ta kasa Reshen Jahar Zamfara, ta kaiwa Mai daraja Gwamna Hon. Dr. Abdulaziz Yari Abubakar 21/03 ziyara a ofishinsa da ke gidan gwamnatin Jahar Zamfara.
Ganawar dai ta samu halartar uban wannan kungiyar na kasa Mataimakin Gwamnan Jahar Zamfara Malam Ibrahim wakkala Muhammad Liman (wanda kacokan shi ne, Wanda ya hada wannan Ganawar) Kwamishinoni shuwagabannin Kungiyar da 'yan Jaridu.
Kacokan dai wannan Ziyarar mun kaiwa mai Girma gwamna ita ne domin Mika Mika sakon wasu daga cikin koken talakawan Jahar Zamfara, tare da taya shi murnar lashe zaben GWARZON SHEKARA munka Shirya.
Shugaban Kungiyar reshen Jahar Zamfara, Comr. Hafizu Balarabe Gusau ya Jinjinawa Mai Daraja Gwamna akan yunkurinsa na shinfida Tituna a Jahar, Da giggina makarannin da sunka lalace, da kuma yadda ya ke Gudanar da mulkin ba tare da cin zarahin 'yan adawa ko masu sukar gwamnatin ba.
Haka zalika kungiyar ta nemi a kawo wa Al'ummar Jahar Zamfara dauki ta hanyoyi da dama.
A lokacin da ya ke jawabi Gwamna Abdulaziz Yari ya yaba matukar gaske bisa ga wannan ziyarar da kungiyar ta kawo mashi. Dan haka Gwamnan ya ce Gwamnatin jahar zamfara zata bullo da hanyoyin da za su taimaka wurin Isar da koken al'umma zuwa ga Gwamnati.
Daga karshe. Gwamna Abdulaziz ya baiwa Uwar Kungiyar reshen Jahar Zamfara naira million biyu tare da alkawarin Mota Bus mai daukar mutane 18.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau PRO I MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA
Post Top Ad
Responsive Ads Here
Wednesday, 21 March 2018
Home
Unlabelled
KUNGIYAR MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA TA GANA DA GWAMNAN GWAMNONI A YAU
KUNGIYAR MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA TA GANA DA GWAMNAN GWAMNONI A YAU
Post Bottom Ad
Responsive Ads Here
Author Details
Templatesyard is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates which are professionally designed and perfectlly seo optimized to deliver best result for your blog.

