Duk da iƙirarin da ake yiwa mulkin dimokaraɗiya na cewa; "Mulki ne na Al'umma da ake yi dan al'umma" Amma a Jahar Zamfara ba Haka abun ya ke ba. Domin su kansu 'yan majalissar jahar Zamfara da nauyi ya rataya kansu na sauraren koken jama'a tare da Tabbatar da abunda Al'ummarsu ke so, shi ne gwamnatin jahar ke yi. Sai dai kash! Ba haka abun ya ke ba, a Jahar Zamfara.
Domin Mafiya yawansu ma su ba ta talakan da ya zaɓe su suke yi ba, kullum gurinsu kawai, Mene ne, za su tara. Hasalima da wahala ka ga sun fitar da ƙudurin da zai taimaki Al'ummar Jahar Zamfara, sai dai wanda zai taimaki gwamnati mai mulki ko su kansu. Ba zan manta wani sauraren jin ra'ayin jama'a da sunka taɓa gayyatar wasu ɗaiɗaikun ƙungiyoyin sa-kai a 2017 ba, Wanda Ƙungiyar MURYAR TALAKA RESHEN JAHAR ZAMFARA na cikin ƙungiyoyin, ni kaina ina cikin masu halartar taron wanda na daɗe ina takaicin yadda zaman ya kasance da kuma ma mau'du'in da ake sauraren jin ra'ayun jama'a akansa. Wato dokar daidai aikin masu KEKE NAPEP (Mashin mai Kafa uku) Wanda kwata-kwata ba wani alfanu da wannan dokar za ta yi ba. Duk da cewa an tattauna akan dokar sama da shekara daya Baya, amma har yanzu ba mu ma San isalinta, ba. Wannan Kenan!
Duk wani ɗan Najeriya ya san rigimar da ta kaure tsakanin gwamna mai ci a yanzu da 'yan majalissar, inda sunka ta ihun cewa wannan rigimar ta faru ne, sanadiyar yunkurin gwamnan na takurawa talakkawan Jahar. Wanda maganar gaskiya sun yi wannan faɗan ne, Dan kawai kare muradun aljihunansu. Hujja akan haka daga ranar da aka cika masu aljihunan nasu shi ke nan. Sunka yi shiru. Duk wani Abunda za a yiwa talaka ba zaka taɓa jinsu ba. Hasalima ko 'yan majalissar tarayya za su yi wa wani dabtarin doka gyaran fuska in za su turo shi a Jahar Zamfara, domin neman amincewar majalissar jahar, komi alfanunsa ba za ka ji sun amince da shi ba.
A madadin hakan sukan jefa shi ne a kwandon shara, ko kuma su rubuta kawai ba su amince ba, Kai tsaye hujja a nan ita ce; ƙungiyoyinmu na matasa mun yi ta yin gangami akan dokar rage shekarun 'yan takara, (Not too young to run bill) Wanda a lokacin mun yi ta gangamin neman su amince da shi, har wasiƙu munka rubutawa dukkanninsu na goyon bayanmu a kan kudurin. Amma daga ƙarshe jahar zamfara na cikin jerin jahohin Najeriya da ba su amince da kudurin ba, Wanda Wallahi kudurin Al'ummar Jahar shi ne, a canza amma sunka tsaya kan ra'ayinsu.
Kwatsam! Sai yanzu ga maganar baiwa ƙananan hukumomin 'yancin cin gashin kai Wanda kuduri ne, mai matukar muhimmancin gaske ga Al'ummar Najeriya musamman talakawa ba Zamfara kurrum ba. Amma ƙiri-ƙiri waɗannan bayin Allah, sun fara yiwa talakawan jahar zagon ƙasa, sun fara biyar Masarautu, wai suna sauraren jin ra'ayin jama'a, Wanda a karkashin kasa, ba gaskiyar abunda su ke yi Kenan ba. Ganin yanzu ma muna hasashen sun kai ƙarshen cewa ba za su amince da kudurin ba, ganin gwamnatin Jahar ba ta da ra'ayin baiwa kananan hukumomin 'yancin gashin kai.
Dan Haka muna amfani da wannan damar mu yi kira ga ita kanta gwamnatin Jahar ta Zamfara, ƙarkashin jagorancin Gwamna Abdul'azizu Abubakar Yari, Da Kakakin majalissar dokokin Jahar Zamfara Rt. Hon. Sanusi Garba Rikiji da dukkannin 'yan majalissar dokokin Jahar Zamfara da su sani cewa; mu al'ummar Jahar Zamfara, ra'ayinmu shi ne; baiwa kananan hukumomi 'yancin gashin kai. Domin baiwa ƙananan hukumomin 'yancin kai zai taimaka matukar gaske wajen sauƙaƙawa mu talakkawan Jahar, Wahalar rayuwa. Domin shuwagabannin ƙananan hukumomin su ne, a kusa da mu.
Dan muna Kira gare su yi gaugawar amincewa da wannan kuduri, domin shi ne ra'ayinmu.
A hannu ɗaya kuwa, muna kira gare ku kamar yadda munka saba, rubuta maku, ku yi gaugawar yi muna dokar da za ta hana Cacar nan ta zamani da ake yi lungu da sako wato BET9JA da ta zamar wa matasan Jahar Zamfara Babbar masifar da a gaba za ta zamar muna ƙarfen ƙafa Ganin yadda matasa sunka fara sace-sace domin neman kuɗin yinta, haka zalika ko a Watanni baya wani matashi ya kashe kansa sanadiyar bai yi nasara ba. Ko ba komi dai cacar ta sabawa koyarwar addininmu da al'adarmu. Kuma sherinta ya fi amfaninta yawa matuƙar gaske, Dan haka ba mu ƙaunar Matasanmu na yinta.
Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Muryar Talaka Reshen Jahar Zamfara) 08069807496
18-3-2018

