GAGARUMIN GANGAMIN NEMAN KARE RAYUKKA DA DUKIYOYIN AL'UMMAR JAHAR ZAMFARA ZAI GUDANA A GOBE ALHAMIS CIKIN GARIN GUSAU! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Wednesday, 9 May 2018

GAGARUMIN GANGAMIN NEMAN KARE RAYUKKA DA DUKIYOYIN AL'UMMAR JAHAR ZAMFARA ZAI GUDANA A GOBE ALHAMIS CIKIN GARIN GUSAU!







Idan Allah ya Kai mu gobe Alhamis 10-5-2018 Hadin kan Matasa na jahar Zamfara za mu yi gangami a babban birnin Jahar Zamfara wato Gusau.

A lokacin gangamin da zai Fara Daga karfe 8:30 na safe a babban masallacin idi da ke Gusau, za mu mikawa mai Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau, gwamnan jahar Zamfara, 'yam majalissarmu na jahar kokenmu.



Kacokan a gun gangamin ba za mu dauki ko Kare ko mu zagi wani ko bakar magana ba za mu yi zuwa ga wani ba. Illa iyaka za mu yi kira NE na a kawowa jaharmu ta Zamfara dauki daga Gwamnatin tarayya. Ganin kullum kisanmu ake yi, ba kakkautawa. Ana satar dukiyoyin al'ummar karkara.

Muna rokon Allah ya sa wannan gangamin ya zama silar kawo Jami'an Tsaro a jahar Zamfara tare da ba su ikon kawo zaman lafiya a jahar Zamfara.


Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau . Jami'in Hulda Da Jama'a Kungiyar Muryar Talaka Ta Kasa Reshen jahar Zamfara

9-5-2018

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here