GIDAUNIYAR CIYAR DA BAYIN ALLAH TA SHIGA GARIN KASUWAR DAJI.... - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 26 May 2018

GIDAUNIYAR CIYAR DA BAYIN ALLAH TA SHIGA GARIN KASUWAR DAJI....

Gidauniyar ciyar da bayin Allah a watan azumi ta mai Daraja mataimakin gwamnan jahar Zamfara. Malam Ibrahim Wakkala Muhammad Liman. wadda kacokan an assasata ne domin ciyar da bayin Allah Dari biyar-biyar kullum, Tun Fara aikin Gidauniyar ta kaddamar da aikinta a Babbar Tashar Motar GUSAU, Mada, WANKE da ke nan  karamar Hukumar Gusau. Wanda ta  cigaba da bada abinci da ruwan sha pure Water. A assibitin Samuru. Tare da assibitin Farida da ke Gusau.
Jiya Kuma ta shiga a cikin garin KWATARKWASHI, a karamar Hukumar BUNGUDU. Inda Gidauniyar ta ciyar da bayin Allah 500 kamar yadda kullum mu ke yi.

Yau Kuma Gidauniyar ta shiga garin kasuwar Daji da ke cikin karamar Hukumar Kaura Namoda, inda ta ciyar da mutun Dari biyar kamar kullum. Insha Allahu zuwa gobe za mu hari wani garin da ke jahar Zamfara. A kokarin Gidauniyar na shiga lungu da Sako na jahar Zamfara domin bayar da tallafi a wannan watan 

Allah ka Sanya albarka a wannan aikin. Tare da Kai ladar aikin a Mizanin mai daukar nauyin aiki.

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here