RASHIN TSARO: MAJALISAR DOKOKIN JAHAR ZA TA AIKAWA MINISTAN TSARO DA WASIKAR NEMAN DAUKI AKAN TASHE-TASHEN HANKULAN DA KE FARUWA A JAHAR. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 26 May 2018

RASHIN TSARO: MAJALISAR DOKOKIN JAHAR ZA TA AIKAWA MINISTAN TSARO DA WASIKAR NEMAN DAUKI AKAN TASHE-TASHEN HANKULAN DA KE FARUWA A JAHAR.

Lura da yadda ake samun karin tabarbarewar harkar tsaro a jihar Zamfara, majalisar dokoki ta amince da a aikawa ma’aikatar tsaro da wasikar neman karin dauki saboda yadda ake ci gaba da samun hare-haren 'yan fashi.

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta bai wa sakatariyarta iznin ta rubuta wasika zuwa Ministan tsaro, Mansur Dan Ali, kan yadda hare-hare ke salwantar da dumbin rayukan jama'a a yankin.

Jaridar Punch wacce ta ruwaito labarin ta bayyana cewa, majalisar ta yanke hukuncin ne a zaman da ta yi jiya Juma’a.

Daukan wannan mataki na zuwa ne bayan da dan majalisa mai wakiltar mazabar Maru ta Kudu, Alhaji Abdullahi Dansadau, ya gabatar da korafi a gaban majalisar a wani zangon zaman majalisar da ke sauraren bukatu na gaggawa.

Dansadau ya bayyanawa majalisar cewa babban abin damuwa ne ganin yadda mutanen da ba su ji ba su gani ba, suke rasa rayukansu a kullum.

‘Yan majalisar wadanda daukacinsu suka amince da a rubuta wasikar sun kuma amince da a nemi karin dakaru a jihar domin su kare aukuwar ire-iren wadannan hare-hare.

Yankin jihar ta Zamfara a ‘yan watannin nan, na fama da mahara da ke far ma kauyuka su kashe dumbin jama’a su kuma kwashi dukiyoyi.

Rahotanni sun yi nuni da cewa a farkon watan nan kadai, an kai wani hari a yankin karamar hukumar Maru, inda ‘yan bindiga suka halaka akalla mutane 30 kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito a shafinta. (VOA HAUSA)

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here