Yau bakwai ga watan RAMADAN Rana ta uku da Gidauniyar Malam Ibrahim Wakkala Muhammad Liman take cigaba da ciyar da bayin Allah, inda ta ziyarci garin WANKE da ke a karamar Hukumar Gusau, inda ta rabawa al'umma abinci da kayan marmari tare da ruwan sha, domin tallafa masu a cikin wannan watan na Ramadan.
Gidauniyar dai za ta cigaba da ciyar da al'umma kullum da abinci da sha da kayan marmari har Kashen wannan watan kullum za ta cigaba da shiga lungu da Sako na jahar Zamfara. Babban fatan Gidauniyar Wadda kacokan Jagaban talakawan Najeriya ke daukar nauyinta. Shi ne bayar da tallafi ga al'umma masu Dan karamin karfi Domin sauwake masu samun abun buda baki.



