Gidauniyar Wadda kacokan za ta yi aiki kasa-rika wannan watan, za ta maida hankali ne, wajen yin abinci kullum Daren Allah ta'alla tana rabawa masu Dan karamin karfi a lungu da Sako na jahar Zamfara.
A Cewar Shugaban Gidauniyar Malam Abdullahi Kanoma "kamar yadda ka ga mun ciyar da mutun Dari biyar da abinci da kuma kayan marmari, za a babbar Tashar Motar GUSAU to haka za mu yi a gobe a garin Mada jibi (Laraba) Wanke za mu tafi haka za mu ta zagawa har Karshen wannan watan.
"Kuma kacokan! Mataimakin gwamnan jahar Zamfara, Malam Ibrahim Wakkala Muhammad Liman ne, ya dauki nauyin wannan aikin domin tallafawa masu Dan karamin karfi a wannan watan.
Wanda babban Fatanmu da rokonmu shi ne Allah ya kai ladar wannan aikin a mizaninsa.

