Hakika yau na yi Kukan zucci tare tausayi marar misaltu.
Saboda wata mummunar aika-aika da na ga Gwamnatin jahar Zamfara tana yiwa al'ummar da ke zaune a unguwar Samunaka da ke cikin garin Gusau. Inda aka turo masu motar ture gidaje domin tarwatsa su.
Babban abunda ya fi ba Ni tausayi shi ne; wani dattijo (in kuka bi facebook profile dina za ku ga firarmu da shi Kai tsaye) Wanda barayin shanu sunka yi masa Kat! Tare da tarwatsa masa rayuwa, da kyar ya mallaki gida a Gusau domin ya tsira da rayuwarsa da jikokin da aka bar masa, Marayu. Amma yau an wayi gari Gwamnati da ya kamata ta yi kokarin kawo masu dauki, ita ce ke kokarin Kashe shi. Wanda ya tabbatar Mani duk Gwamnati ta rushe masa gida, to zai mutu ne, kurrum!
Mutun na biyu shi ne wani matashi da ya Kera gida na tsara, duka watansa shida da Mako daya da komawa gidan, bayan ya shafe shekaru uku yana gidan haya tare da shafe shekaru uku yana Gina gidan. Amma dare daya yau an ce ya tashi za a rushe shi. Wanda ya tabbatar Mani da cewa yanzu haka bai san inda zai sanya rayuwarsa ba, domin da buga-buga ya hada gidan, wani lokacinma yakan hana kansa abinci Dan baiwa gidan (in kuka bi facebook profile dina za ku ga firarmu ta bidiyo da shi Kai tsaye) ganin cewa ya yi shekaru takwas da Kare makaranta amma bai samu aiki ba, Kuma hakan bai sa ya zama cima kwance ba, ya tabbatar da ko wajen da matarsa ma za ta kwana, bai da shi. yanzu sai dai ta raba. Duk da ni'imar da Allah ya masa. Na Tabbatar wannan matashin zai iya yin komi a wannan halin da ya shiga!
Duk da cewa Akwai wasu tsofaffi mata da yara kana da na tarar suna ta birgima a kasa, wadanda wasunmu ma a lokacin sun zauto, domin fatansu na karshe Kenan aka raba su da shi. Sai kuma wani matashi da ba Ni tunanen ya Kai shekaru talatin da na ga yana Kaiwa da komowa yana fadin wallahi sai sai turmuza su duka lahira shi da gidansa. Domin guminsa NE, da wahalar gaske ya samu kudin Gina wannan gida dare daya a ce za a rushe shi tare da maida shi turbaya, wallahi ba za ta sabu ba Wai bindiga a ruwa! Wannan kenan.
Duk da cewa ba wani Wanda ya ke iya ja, da Gwamnati, haka Duk wani fili da ke jahar Zamfara mallakar Gwamnatin jahar ne, Duk inda ya ke, Sai dai in ta ara maka, bayan ka biya 'yan matsabbai ko kyauta na 'yan shekaru da ke tukewa....
Hakika wannan unguwar kamar yadda aka tabbatar Mani filin Gwamnati ne, da ta kebe domin yin wani amfani da shi, Tun lokacin mulkin soji bayan samuwar jahar. Wanda gwamnatoci sun yi ta yunkurin alkinta shi, Sai dai damar ce, ba ta taso ba. Wanda wasu azzalumai daga cikin Gwamnatin da wasu azzaluman dillalai suka yi ta sayarwa talakawa shi.
Wanda na tabbatar duk wanda ya san filayen nan na Gwamnati ne, wallahi ba zai saye shi, har irin hakan ya faru kansu ba.
Dan haka muna amfani da wannan dama domin yin kira ita Gwamnatin jahar Zamfara mai taken addininmu al'ummarmu, da ta dauki matakin damko wadanda sunka yi cuwa-cuwar cutar da wadannan al'umma Naki tare da daukar kwakkwaran mataki akansu, Domin ya zama izna ga mu 'yan baya.
Haka zalika muna kira ga ita wannan Gwamnatin mai adalci da ta dubi yuyuwar musanya masu wannan wuri da wani a cikin yalwar arzikin da Allah ya yi mata, tare da taimakon masu gidajen a wurin Dan dawo da rayuwarsu kan turba natsattsiya.
Daga karshe muna rokon Allah ya sa wannan koken namu ya kai ga kunnuwan wadanda munka yi domin su.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Muryar Talaka Ta Kasa Reshen Jahar Zamfara)

