KUNGIYAR DALIBBAN JAHAR ZAMFARA (NUZAMSS) TA YIWA FARFESA BILBIS TA'AZIYA. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Tuesday, 1 May 2018

KUNGIYAR DALIBBAN JAHAR ZAMFARA (NUZAMSS) TA YIWA FARFESA BILBIS TA'AZIYA.


A yau Talata 1-5-2018 kungiyar Dalibban jahar Zamfara (Nuzamss) ta kai gaisuwar ta'aziya ga prof. Lawal Suleiman Bilbis. A gidansa da ke Bilbis.


Tawagar kungiyar Wadda ta Kunshi. Hon. Mahi Abdullahi (DG scholarship Zamfara State)  Shi ne Wanda ya Jagoranci Kungiya tare da rakiyar mukkadashin Shugaban kungiyar Kuma Maitaimakin Shugaban kungiyar Muhammad Tambura,  Sakataren kudi na kungiyar  Nasiru Nesta tare da tsohon shugaban kungiyar  M Z Mayana.



 Ziyarar dai kacokan sun kaita ne domin jajantawa ga Shehin Malamin Kuma uba ga dalibban jahar Zamfara. Akan rashin da ya yi na mahaifiyarsa a jiya litinin.



A lokacin da tawagar ke jawabi a gun wannan ta'aziyar ta bayyana jimaminta akan wannan babban rashin, ganin yadda mahaifiyar ta yi aiki tukuru wajen bayar da tarbiya ta gari ga 'ya'yanta har Allah ya nuna mata ta haifi farfesa wanda ke tallafawa dalibbai ta Kowane hauji. Daga karshe sun roki Allah ya gafarta mata Dukkanin kura-kurranta ya sa aljanna firdausi ce a makomarta, ya kuma baiwa iyalinta ikon jure wannan rashin.


Da yake maida jawabi Shehin malamin ya nuna jin dadinsa Matuka da wannan Ziyarar, ya kuma roki Allah ba su ladar da ke cikin wannan aiki.


Daga: Sashen Kula da shafukkan sada zumunta na kungiyar Dalibban jahar Zamfara. (Abdulmalik Saidu Mai Biredi)

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here