KARANCIN RUWAN SHA A GARIN GUSAU! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Tuesday, 1 May 2018

KARANCIN RUWAN SHA A GARIN GUSAU!



A shekarun baya kusan Duk gidan da ka lega garin GUSAU za tarar da fanfo yana kawo ruwa, da ruwan sun dawo Tiyo kawai mutane su ke sanyawa su cika tsuma-karansu....

Sannu-sannu al'amurran Duk sun jagule, da wahala ka samu gidan da fanfo ke kawo ruwa. Inda MA ruwan ke zuwa dole sai an yi Rijiya an jira ruwan sun taru a Sanya abun Diba a debo Dan amfanin yau da kullum. Wanda hakan na da matukar Illa ga lafiyar al'umma, ganin yadda Rijiyoyin su ke kwana bude,  Kuma ba wankin kirki ake yi masu ba. Hasalima da wahala a WANKE su. Sai dai a kwashe ayi amfani da su a haka, duk citukkan da kan baje kulinsu a cikin Rijiyoyin.

Wata babbar matsalar ita ce, rashin zuwa makaranta ga yara Maza da mata sanadiyar zuwa neman ruwa.  Domin a lokacin da yaran su ke wajen neman ruwan kamata ya yi suna makaranta, amma ina.

Dan haka muna kira ga Gwamnatin jahar Zamfara, mun tabbatar da Gwamnatin ta yi kokarin sawo Injinonin da ke samar da wutar lantarki a babban gidan ruwan GUSAU. To Sai dai inda gizon ke saka, har yanzu ba wani sauyi da aka samu, kullum ma gwamma jiya da yau.

To ina matsalar take?

Ina Injinonin?

Anya ana aiki da su kamar yadda ya dace?

Anya suna aiki?

Shin su ma NE matsalar ruwan?

In ba ita ba ce, ina matsalar take?

Hakika ya kamata Gwamnatin jahar ta yi bincike na musamman domin gano musabbabbin wannan matsalar.

Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau Pro 1 Muryar Talaka Reshen jahar Zamfara 08069807496

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here