KUNGIYAR DALIBBAN JAHAR ZAMFARA (NUZAMSS) ZA TA SHIRYA WA DALIBBAI BITA AKAN KULA DA SHA'ANIN TSARO - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 30 April 2018

KUNGIYAR DALIBBAN JAHAR ZAMFARA (NUZAMSS) ZA TA SHIRYA WA DALIBBAI BITA AKAN KULA DA SHA'ANIN TSARO

Ganin halin rashin Tsaro da kusan kullum jahar Zamfara ke Kara fadawa, dama Najeriya baki daya, ya sa kungiyar Dalibbai 'yan assalin jahar Zamfara (NUZAMSS) ta ga ya dace ta jawo hankalin Dukkanin shuwagabannin jahar dama na Kasarmu Najeriya baki daya,  da su taka muhimmiyar rawa wajen  ganowa dama shawo kan matsalar Tsaron da ta ki ci taki cinyewa.

Babban abunda ya jawo hankalin kungiyar ga shirya wannan gangamin ga dalibbai shi ne Ziyarar da Maitaimakin Shugaban kungiyar na daya Muhammad Yahaya Tambura tare wasu shuwagabannin kungiyar suka kaiwa wasu daga cikin hukumomin Tsaron Zamfara.

Da kuma wata  Kasida da Shugaban kungiyar na Jaha Comr. Sen. Mubarak Garba ya Gabatar a wata tattaunawa kan matsalar tsaro da Hukumar  National Institute for research and developmental studies and security agencies ta shirya a ranar  25th April 2018, a fadar Gwamnatin jahar Zamfara. Inda ya yi Karin haske akan irin gudunmawa da dalibbai za su iya bayarwa domin samar da Tsaro a jaha ba zai iya misaltuwa ba.

Taron bitar zai mayar da hankali ne, akan fadakar da Matasa Akan yada za su yaki ta'addanci a waka-junansu. Tare da dabaru da za su iya amfani da su Dan  gane Dan ta'adda da dakile ta'addancin Tun kafin ya Kai ya yi Illa ga al'umma.

Bitar za ta kunshi, Kasidu daga bangarori na jami'an Tsaro,  Farawa da  kwamishin 'yan Sanda, darakta SSS, kwamandan Jami'an Tsaron fararen kaya (NSCDC) da sauran jami'an Tsaro da ke yaki da 'yan ta'adda. Tare da nunawa Matasa hanyoyin da za su bi domin maganin matsalar tsaro.

 

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here