KUNGIYAR DALIBBAN JAHAR ZAMFARA (NUZAMSS) TA KAI ZIYARAR SADA ZUMUNCI GA JAMI'AN DSS DA NSCDC.... - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Thursday, 19 April 2018

KUNGIYAR DALIBBAN JAHAR ZAMFARA (NUZAMSS) TA KAI ZIYARAR SADA ZUMUNCI GA JAMI'AN DSS DA NSCDC....




A yunkurin kungiyar na karfafa zumunci, da fahintar juna a tsakanin 'ya'yan kungiyar da masu rike da madafon iko a jahar Zamfara. 

kungiyar ta aminta da ta Fara ziyarce-ziyarcen domin bayyana manufofin kungiyar da kuma kudurorin kungiyar ta dalibban jahar Zamfara. Ga jami'an Gwamnatin Jahar Zamfara 

Cikin iyawar Allah kungiyar ta yi nasarar zama da muhimman jami'an Tsaron jahar Zamfara 

Farawa da daraktan SSS, Alhaji Hadi Sudawa Tare da mataimakinsa  A shalkwatar Hukumar ta  jahar Zamfara da ke Gusau.

Sai kuma Shugaba Hukumar jami'an Tsaron fararen kaya (NSCDC) D.A Abi tare da tawagar ma'aikatansa. A ofishinsa  

Ziyarar Wadda mukadasshin Shugaban kungiyar Dalibbai ta jahar Zamfara Kuma mataimakin Shugaban na jaha Comrade Muhammad Yahaya Tambura ya wakilta. Ya bayyana manufofin kungiyar da kuma kudurorin da kungiyar ta sa a gaba. Tare da Gabatar da sabbin zaben shuwagabannin kungiyar na jaha. 

A lokacin da jami'an ke maida jawabi, sun nuna matukar jin dadinsu da wannan Ziyarar, tare da  kira ga kungiyar da ta zama uwa ta gari wajen yaki tukuru da zai kawo zaman Lafiya a Waka junan yayanta. Domin samun cigaba mai Dorewa da kwanciyar hankali a jahar Zamfara.

Ziyarar da ta samu rakkiyar Maitaimakin Shugaban Kungiyar na 1 da Jami'an Hulda da Jama'a na 1 da na 2 Shugaban kungiyar Dalibbai Zamfarawa na Jami'ar Usman Dan fodiyo da sauran Sanatoci.

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here