ABUNDA EFCC TA YIWA MUKTAR LAMARAN YERO! YA YI DAIDAI DOMIN BA FIN SAURAN TAKWARORINSA YA YI BA! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 2 June 2018

ABUNDA EFCC TA YIWA MUKTAR LAMARAN YERO! YA YI DAIDAI DOMIN BA FIN SAURAN TAKWARORINSA YA YI BA!

Ni ba lauya ba ne, kuma ba Ni da ilimi Akan aikin lauya da ma Shari'ar baki daya balantana in ce, an keta haddin Tsohon Gwamnan Jahar Kaduna Muktar Lamaran Yero. Na watsa shi a duniya tare da allon da ke nuna cewa ana ZARGINSA da ya karbi hanci da rashawa. Duk da ba tabbatar masa da laifinsa ba.



Sai dai ni a matsayina na Dan kasa, zan iya tofa albarkacin bakina, kamar yadda na ke da damar haka a duk wani Abu da Shari'ar ba ta katange ni gare shi ba.


Ya kamata mu yi nazari mai kyau!

Kusan Duk ofishin 'yan sandar jahar da ka leka a kasar nan za ka tarar da hotonan mutane da aka zarginsu da aikata wata aika-aikar har suka tafi hannun 'yan SANDAR!

Duk A lokacin da su ke gunsu ba masu laifi ba NE, Sai kotu ta tabbatar masu da laifin amma hakan bai hana a dauki hotonsu da kayan da ake zargin sun sata ko matara Kama da haka, za a Sanya hotonansu duniya na cigaba da kallonsu . Wannan kenan!

Duk wani mai cece-ku-ce Akan wannan hoton ina ganin akwai daya a cikin wadannan a tare da shi.

Ko dai ya San Gaskiya Sak! Amma ya rike Karya,
Ko kuma ya kasance baida ilimi Akan yadda EFCC ke gudanar da aikinta. Domin na tabbatar duk mai biyar shafin facebook na wannan Hukumar zai ga yadda kusan kullum su ke doro hotonan mutane da ake zargi da aikata ba daidai ba. Wasu sun yi babban laifi wasu Kuma laifin bai taka-kara-ya-karya ba. Amma zaka tarar sunansa baro-baro da laifin da sunka yi ana yadawa duniya Kai tsaye, kamar yadda aka yi kan Malam Lamaran Yero.

Wannan na nuna cewa Hukumar tana aiki kamar yadda yan sanda ke a ofisoshinsu.


Amma dan dai son Kai irin namu mun yi caaa! Wai EFCC TOZARCI ne da cin mutunci ta yi masa..

Sai dai abunda a ban sani ba, na San yana gwamna, yana da rigar kariya ta musamman da zai gurfana a gaban kuliya ba.

Yanzu Kuma ya sauka, ana tuhumarsa, Wanda hakan ma NE, ya sa ya je ga EFCC, Anya kuwa an yiwa sauran takwarorinsa adalci?

A cikin wannan rubutun na doro hotonan mutane da wasu abinci ma ne su ke nema Dan talauci akwai wasu sunka tsiri zamba, wannan Hukumar ta Dora hotunansu da abunda ake tuhumarsu da yi

Haka zalika shi kansa LAMARAN ba Wai cewa aka yi an tabbatar da laifinsa ba ne. Hoton tuhuma aka dauka kuma kai mai kummar baki ka  je ofisoshin 'yan sanda, kullum haka suke wa wadanda ake tuhuma kafin kai su kotu. Sau nawa kuma ake bayyana 'yan fashi da makami a gaban 'yan jarida, a baza hotunansu kuma har ma a yi magana da su kafin a je kotu. Ko Evans mai garkuwa da mutane da aka kama, an baza kolinsa ga yan jarida.


Dan haka in dai TOZARCI ne ko take hakkin Dan Adam NE, to ba akansa aka soma ba, in Kuma har ya haramta a kudin tsarin mulkin kasa, to Alhamdulillahi Talakan Najeriya da a kullum ake walakantawa ya samu sa'ida. Domin an Fara taba manya zai samu garkuwa kenan!


Dan haka ina amfani da wannan damar in yi roki rokarwa shi lamaran Yero mafita.


Allah in wannan bawa naka na da Sanya hannu a wawurar kudin talakawan Najeriya ka baiwa jami'an EFCC damar gano badakalar tare da hukunta shi daidai laifinsa!

Allah in Kuma bai da sa hannu Allah ya yi masa mafita da sauran makaraban da aka Kama su da shi.

Ya Allah ka Kare mu Daga fuskantar TOZARCI na duniya uwa uba na kiyama. Allah ka sa mu karshe mai kyau.


Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau

2-6-2018




Post Bottom Ad

Responsive Ads Here