Daruruwan 'yan gudun hijira Maza da mata, yara kanana da kuma tsofaffi sunka durfafo garin garin GUSAU a yau, Jumu'a. Domin gujewa wasu miyagun 'yan ta'adda da za su shigo a kauyukkansu.
'yan gudun hijrar dai sun Fito ne, Daga yankin jangeme zuwa Magami.
Duk wani yunkuri namu na zantawa da su kamar yadda ya dace yacitura. Saboda Tsoro da ke tattare da su. Domin tashin hankali da ke tattare da zuciyoyinsu, Wanda ya sa mata da yaran cikinsu ke ta kuka.
Yanzu haka dai sun bar bayan gidan marigayi Ummaru Shinkafi da ke GRA GUSAU a yunkurinsu na neman jami'an TSARO DA ZA su raka su zuwa kauyukkansu tare da ba su kariya. Sai dai tuni Shugaban karamar Hukumar mulkin Gusau, Hon. Ibrahim Umar Tanko ya zo gunsu har ya ba su kudin shan mai. Tare da daukar matakin da ya dace, Duk dai yanzu da na ke wannan rubutun ba wani jami'in Tsaro ko jami'in Gwamnati da ya zo gunsu.







