Yan siyasa a lungu da Sako na jahar Zamfara suna cigaba da ribibin Baiwa Malam Ibrahim Wakkala Muhammad Liman (Sarkin Malaman Gusau ) Kuma mataimakin gwamnan jahar Zamfara, gudunmawowin motoci, Babura da sauran kayayyankin yakin neman zabensa.
Na baya-bayan nan shi ne Alhaji Abubakar Jatau Kanoma ( Sarkin Bauran Maru) Wanda a cikin Daren yau Alhamis 28-6-2018 ya bada gudunmawar mota 406 mai lamination, Riguna 700, Hulluna 700 da Posta kwafi 5000.
Sarkin Bauran dai Can baya ma ya baiwa mataimakin gwamnan gudunmawowi domin mara masa baya tare da karfafa shi domin neman gwamnan jahar Zamfara a 2019..
A lokacin da ya ke maida jawabi
Maitaimakin gwamnan jahar Zamfara, ya nuna jin dadinsa Matuka da gaske da wannan kyautar, Kuma ya nuna cewa hakan ya nuna cewa akwai masu nuna soyayya Dan Allah.
Daga karshe mataimakin gwamnan ya bayyana cewa mutane irin Bauran Maru na Daga cikin dubban mutanen da ke kara masa karfin guiwa wajen neman kujerar gwamnan a 2019.

