Na yi Mamaki matukar gaske da na ji daga bakin mai taimaka maka a bangaren watsa Labarai!
Cewa ka jagoranci gwamnoni 11 domin jajantawa ga al'ummar jahar PLATEAU Akan rashin mutane 86 da aka yi!
Na tabbatar da cewa wannan Ziyarar ta cancanta, Sai dai wani hanzari ba gudu ba. Yau shekarunka 7 da kwana 29 Akan karagar mulkin jahar Zamfara!
Kusan Tun da ka hau mulki duk Daren Allah ta'alla Sai an Kashe mutanenka!
Duk da an kawo jami'an Tsaron da zan iya kira tsiraru, ba wai Dan rashin kwarewa ko TSoro ba, Sai dan karanci da kuma rashin kayan aikin da za su fuskanci 'Yan ta'addan Wanda ko yau na shiga wani kauye a cikin karamar Hukumar Kaura wanda sunka tabbatar mini da cewa ba Daren Allah ta'alla da dayan mazajen garin, ke kwantawa su yi barci kamar kowa. Dole sukan Mike domin kariyar Mataye 'ya'ya da masu rauni da tsofaffi tare da kokarin ganin sun Kare dukiyarsu daga sata ko daukar rayukkansu daga 'yan ta'adda da su ke zaman doya da manja tare da su! Wanda sunka tabbatar da cewa, su sai dai su ji Labarin jami'in Tsaro, amma maganar SOJA ko Dan sanda ba a taba kawo masu ba! Wannan kenan!
Mai girma gwamna halin da al'ummarka fa su ke ciki kenan idan muka dauki mutanen Kizara, 'Yar Tasha, baiwar Daji da na baya-bayan nan Tungar haki, an Kashe mutane akalla a wannan aika-aikar, daruruwa. Amma ba daya daga cikinsu da ka taba kiran gwamna daya ya Mara maka baya domin yi masu jaje in ka Debe kashe-kashen Zurmi da ka leka Masarautar tare da rakkiyar Tambuwal da Shema bayan kun dawo Daura daga nan kuma ka tsakke kasar Jamus, wajen yin abunda ni dai da sauran Zamfarawa za mu kira sharholiya. Domin ba mu san dalilinsa, ba.
Sai kuma Yar Galadima da ka yi wa gawarwaki fada.
To har yanzu mu taba ganin ka zo yiwa wasu al'ummar jaje ba, a jahar ZAMFARA. Amma dan abunda zan kira rashin kishi da tausayi, yau ka Kama hanyar Jos wai yin jaje.
Abun tambayar a nan shi ne;
Anya mai Girma gwamna wanda aka yiwa mutuwa yana da zarafin shiga jagorantar wasu su je Ziyarar marar Lafiya, kafin kawar da gawar mamacinsa?
Anya kuwa, Wanda ya bar gawar mahaifinsa magashiyan ya tafi Ziyarar marar Lafiya da ke ciyon da bai wuce zazzabin wucin-gadi ba, ya kyauta?
Tabbas al'ummar jahar Zamfara na cikin tashin hankali marar misaltuwa, Wanda daya daga cikin abunda ya jefa mu cikin wannan mummunan halin shi ne, nuna halin ko in Kula da gwamnatinka ta yi da sha'anin Tsaro. Dan haka muna cigaba da kira ga ka Dena Duk wasu yawace-yawace irin wadannan ka dawo gida ka rungume mu, matsalar da tafi karfinka ka nusar da Gwamnatin tarayya shi ne mafi a'ala.
Allah muna rokonka ka arzurtamu da zaman Lafiya Mai Dorewa a jahar Zamfara tare da Najeriya baki daya.
Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau
29-6-2018

