IN KA SHIGA PDP ZA KA YI BIYU-BABU - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 2 July 2018

IN KA SHIGA PDP ZA KA YI BIYU-BABU


A lokacin da MAS (Tsohon gwamnan jahar Zamfara)  yana cikin jam'iyar PDP, al'ummar jahar Zamfara musamman TALAKWAN JAHAR na kanarsa Matuka! Amma da ya dawo PDP Sai farin jininsa ya rage Matuka!

Kuma haka na ke hasashen zai kasance ga Sanata RABI'U MUSA KWANKWASO!

PDP da APC uwarsu daya ubansu daya, amma yanzu kwankwason yana da tarin magoya baya da na ke tunanen in ka Debe Shugaba Buhari, ba na biyunsa a Najeriya, wajen farin jini.

Amma muddun ya bar APC zai yi hasarar wasu Daga cikin magoya bayansa, da jam'iyar APC ce, abun rikonsu fiye da shi.

Yayin da kuma ita PDPn ba wasu jajirtattun magoya baya zai samu ba, la'akkari da mafiya yawan wadanda zai isko a PDPn  tuni sun yi Nisa da Masu gidajensu, Kuma sonsu ya riga ya yi tasiri  a zukatunsu!

Ina ganin da ka zaunarka a APCn ku ci karenku babu babbaka kafin ta Allah ta yi tasiri Akanku da ya fi maka! Domin shiga PDP ina ganin biyu babu za ka yi!

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau

2-7-2018

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here