Wasu matsafa biyu da ake tuhuma da kashe wata mata ’yar shekara 19 a karamar Hukumar Adabi, Jihar Kogi sun bayyana cewa kafin su kashe ta sai da suka yi mata fyade, sannan kuma suka kara yi wa gawar tata fyade daga baya.
Wani fasto ne mai suna Oluwasegun Otaru na Cocin C&S Aladura, boice of Canaan Temple, tare da abokan tsafinsa biyu, Oluwasegun Samuel da Yakubu Abdulmumini ne suka bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata, a lokacin da Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Kogi ta gabatar da su gaban manema labarai. Haka kuma wadanda ake tuhumar sun amsa laifinsu da cewa sai da suka yanke tafin hannun matar, suka gasa sannan suka cinye, a matsayin wani aiki na cikar tsafin da suke yi domin samun kudi.
An gabatar da wadannan matsafa ne tare da wasu mutum bakwai da ake tuhuma da laifin kashe jami’in dan sanda tare da wasu mutum uku. Otaru ya bayyana cewa da farko dai shi mai wa’azi ne na gaskiya amma daga bisani saboda son kudi sai ya kauce hanya.
Ya bayyana cewa sau biyu yana tono gawarwaki daga kabari domin bukatar tsafinsa da nufin ya yi kudi, amma bai samu kudin ba. Ya ce ita matar da suka kashe mai suna Mercy Moses, shi ne ya shirya yadda za a kashe ta. Ya ce tsafin da suka yi da ita, suna tunanin za su samu Naira miliyan biyu da rabi a ranar.
Kakakin ’Yan sanda a Jihar Kogi, William Aya ya bayyana cewa sun kama wadanda ake tuhumar ne a sakamakon koken da suka samu na bacewar matar da suka kashe. Ya ce mutane biyu da aka fara kamawa, Oluwasegun Samuel da Yakubu Abdulmumini ne suka je wani otel suka dauki wannan mata, suka kai wa shi matsafin a cocinsa. Su ne kuma suka jagoranci ’yan sanda zuwa wurinsa, inda suka kama shi. Ya nuna inda suka rufe sauran sassan jikin mamaciyar. An samu kanta da tafin hannunta.
Su kuwa sauran mutane bakwai da aka gabatar ga manema labarai bisa tuhumar kashe jami’in dan sanda da wasu mutum uku sun hada da Ubile Attah da Abdul Tijjani da Julius Alhassan da Onuche James da Akwu Audu da Shehu Haliru da Amedu Yakubu.
Kakakin na ’yan sanda ya ce an kama su ne a yankin Ejule da Ugwolawo da ke karamar Hukumar Ofu, Jihar Kogi. Ya bayyana cewa har yanzu rundunarsu na ci gaba da bincike kuma da zarar sun kammala, za a gurfanar da su gaban kotu. (Aminiya)

