DOKAR TAKAITA YAWO DA BABURA A JAHAR ZAMFARA, KO DOKAR IYAR DA TARWATSA TALAKAWAN JAHAR? - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 9 July 2018

DOKAR TAKAITA YAWO DA BABURA A JAHAR ZAMFARA, KO DOKAR IYAR DA TARWATSA TALAKAWAN JAHAR?


Kwatsam! Muka wayi gari da jin Labarin Gwamnatin jahar Zamfara ta Sanya dokar Takaita zurga zurga daga karfe shida na Marece zuwa bakwai na safe (6:00pm-7:00Am)

A Duk fadin jahar Zamfara, dokar ta Sanya Duk wani Talakan jahar Zamfara dama masu kishin Jahar suka shiga mummunar demuwa da damuwa marar misaltuwa. Domin babban abun tashin hankali ne, irin garuruwa manya na jahar Zamfara kamar Gusau a Sanya irin wannan dokar, Wanda Sanya ta zai jefa al'umma cikin mummunan halin nakasa da illatuwa marar misaltuwa.

Ganin irin halin da al'ummar jahar suka shiga a shekarun baya da aka Sanya makamanciyar irin wannan dokar, Duk da dokar bata Kai munin wannan ba, amma Illar da ta yiwa al'ummar jahar da walaha su maida ita, a shekaru goma sha biyar masu zuwa.

Da dama daga cikin 'yan Acaba na jahar Zamfara sunyi Hijira ta dole, Wanda hakan ya kawo matukar karancin babu tare da Sanya talakawa cikin mawuyancin hali, Wanda yanzu haka muna fuskantar matsalolin.

Sai kuma mummunar matsalar ita ce; Kashe bangaren kasuwancin jahar wanda Duk wanda ya rayu a jahar Zamfara, a shekarun baya. Yanzu ya shigo jahar zai zubar da kwalle ne, ganin yadda aka samu matukar koma baya.  Wanda ya yi sanadiyar Karewar da dama daga cikin 'yan kasuwar da ke baje hajarsu a cikin dare. Domin mafiya yawan masu sayen kayansu talakawa ne, da kan zo kan babur ko Acaba.

Wani hanzari ba, gudu ba, ina ganin ya kamata mai girma gwamna ya yi Koyi da uban Gidansa wajen tausayin talakawansa wato Senator Ahmad Sani Yariman Bakura, Wanda a lokacin Gwamnatinsa da dama Akan dubi yuyuwar yiwa Talakawansa abunda bai dace, ba. Amma Kai tsaye ya ke danganta abunda da cewa shi aka yiwa abunda Kuma al'ummaraa ne.

Mai girma gwamna, Rana daya, ka Sanya wannan dokar Wadda na tabbatar, kaima ka tabbatar da al'ummarka za su cutu matukar gaske. Wanda a sani na Shugaba adili yana kokarin yin abunda zai faranta rayuwar al'ummarsa ko da kuwa zai tauyu ne.

Kamar yadda ku ke bada fatawar cewa Kuna wannan yunkurin NE, Dan samar da Tsaro a jahar Zamfara. Sai dai abunda har yanzu a ban sani ba, shi ne; wane mataki kuka dauka na tabbatar da cewa wannan dokar ta karade Dukkanin jahar Zamfara?

Domin da dama Kukan kasance Kuna magani NE, daban amma cuta daban. Akan kafa dokar ne, da zummar dakushe 'yan ta'addar da kan Kashe da yin garkuwa da mutane a cikin Kauyukka na jahar Zamfara. Amma can ainahin inda matsalar take Sai ka tarar suna cigaba da cin karensu babu babbaka. Amma nan cikin. Manyan Garuruwan jahar zaka tarar kullum ana wasan kura da masu baburan.

Tabbas mai girma gwamna kamar yadda ku ke da'awar cewa kun Sanya wannan dokar Dan Kare rayukkan jama'a to ya kamata kafin Sanya ta, ku dauki matakin samar da wadatattun kekuna masu kafa uku, domin saukakewa al'ummar jahar Zamfara sufuri a yayin da wannan dokar ke cigaba da guda. Ko ba komi mun San gwamnatinka tana da tashin wadannan kekuna da ta kebe suna cigaba shan kashin ruwa, suna lalacewa. Wanda bayar da su shi ne mafi a'ala ga al'ummar jahar Zamfara.

Daga karshe muna amfani da wannan damar wajen rokon Allah ya baiwa jami'an Tsaron ikon murkushe 'yan ta'adda a Duk inda su ke tare da  kawo muna dawwamammen zaman Lafiya Mai Dorewa.

Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

9-7-2018

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here