SANYA DOKAR TAKAITA YAWO DA BABURA: AKWAI MATUKAR BUKATAR TALLAFIN BABURA MASU KAFA, UKU A JAHAR ZAMFARA DAGA 'YAN SIYASAR JAHAR. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Tuesday, 17 July 2018

SANYA DOKAR TAKAITA YAWO DA BABURA: AKWAI MATUKAR BUKATAR TALLAFIN BABURA MASU KAFA, UKU A JAHAR ZAMFARA DAGA 'YAN SIYASAR JAHAR.



Ganin yadda al'ummar jahar Zamfara, mu ke matukar shan wahala wajen samun ababen hawa, Tun baya Sanya dokar takaita yawo da Babura da Gwamnatin jahar ta yi. Wanda saboda karancin Babura masu kafafu uku da al'ummar manyan Garuruwan jahar Zamfara mu ke fama da shi, Wanda hakan kansa, mutane su yi tafiya mai Nisan gaske, da tafin kafarsu. Saboda karanci da rashin wadatar wadannan Baburan. Dan haka muna amfani da wannan damar mu yi kira ga Gwamnatin jahar Zamfara, 'yan Siyasarsu da masu kishinmu, masu hannu da shuninmu da ke tausayin talakawansu, Dan Allah ku yi kokarin wadata al'ummar jahar Zamfara da Babura, masu kafa uku.

Domin sauwake muna yin sufuri cikin walwala tare da bunkasar kasuwancinmu. Kasancewar saboda karancin wadannan Babura ya sa da dama daga cikinmu mu ke Rufe guraren kasuwancinmu da wuri dan neman abunda zai Kai mu gida ko takawa a kafa.

Daga karshe muna rokon Allah ya sa kokenmu ya kai ga kunnuwan wadanda munka yi domin su. Domin dai wallahi al'ummar jahar Zamfara mu na matukar bukatar wadannan Babura.


Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau

17-7-2018

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here