Dokar Wadda Gwamnatin jahar Zamfara ta kafa domin ta taimaka wajen takaita aika-aikar kisan gillar da ake yiwa al'ummar jahar Zamfara. An Sanya dokar ne a ranar 9-7-2018 wanda a karkashin dokar an haramtawa Dukkanin al'ummar jahar Zamfara Hawa Babura daga karfe shida na Marece zuwa bakwai na safe (6:00pm-7:00am) a lungu da Sako na jahar Zamfara baki daya.
Wanda muddun da ainahin manufar takaita aikin assha din ne, aka kafa ta za mu yi san barka duk da tagayyara mu da dokar ta yi. Ranmu ya fi tagayyarar.
To sai dai inda gizon ke sakar, aikin mafiya yawan jami'an Tsaronmu. Na yin aiki ba dan kawo sauyi ba, Sai dai dan tara matsabbai a hannayensu! Tare da aiki kan marar uwa a gindin murhu, tare da gyale shafaffu da mai.
Ina ganin Gwamnatin jahar Hakika ta yi bakin kokarinta na samar da motoci ga jami'an Tsaron, in ko haka ne, banga dalilin Hawa babur ko ya yi kabu-kabu ga jami'in Tsaro ba. Dan dai yana shafe da mai....
Ina ganin in dai jami'in Tsaro zai sanya kayan gida, ya shakata da babur dinsa ba tare da an ce masa kanzil! Ba, to TALAKA ya shiga uku, Kuma ina ganin aihanin manufar dokar ba zata cika ba. Domin an dade ma ana zargin wasu jami'an tsaro da hannu wajen aikata wasu ayukkan assha! Wanda a nan ma sukan iya kai bantensu!
Kullum ina bakin titi Tun daga lokacin da dokar kan Fara har kusan sha biyun dare. Amma abunda ke daure muna kai, shi ne. Shida da mintinuna na yi za ka ga gari ya cike da jami'an Tsaron. Ta ko ina neman 'yan Acaba na sauran mahaya Babura ake yi, wani lokacin har da itace su jama'an Tsaron su ke amfani. Dan kamawa tare da tabbatar da dole sai an bi dokar. Sai dai kash! Da zarar an Dan ja sai ka rasa inda jami'an Tsaron su ka shige. Domin da wahala ka ga daya daga cikinsu in tara ko goma na dare ta yi, zuwa sama, (daidai lokacin da aka fi bukatar yawansu, domin dakile aika-aika) Wanda barayi sukan yi amfani da daukewar sawun al'umma wajen balle shagunan al'umma. Wannan kenan!
Sai kuma wata matsalar ita ce, yadda za ka tarar ana farautar babur din mutane fiye da masu baburan. Wanda ina ganin tunda dai farautar mai laifi ake yi, ba wai ainahin laifin Hawa babur din ba, ana tunanen duk wanda ya hau babur a wannan lokacin Dan ta'adda ne yana dauke da miyagun makamai wanda ya kamata a tabbatar an Kama shi, Domin bincikensa ko ya boye ko yana dauke da kayan ta'addancin nasa. Amma ina babur din dai ake so a Kama shi kuma sai ya yi gaba. Da safe ya zo beli, ka ga kenan an yi baya ba zane, domin in Dan ta'adda ne, zai boye makamin da ya ke dauke da shi, kafin zuwa karbar babur din nasa.
Wani babban abun daure kai shi ne, idan ka Tambayi wadanda ake cigaba da yiwa kisan dauki dai-dai tare da sace masu dukiya a cikin Kauyukka, wadanda a tsammaninmu Dan su ne aka Sanya ita wannan dokar. Sai ka tarar dokar ba ta aiki a gunsu, kwata-kwata. Za su iya Sheda maka ma, su ko jami'an Tsaron ma ba su da su kwata-kwata balantana su hana hawa babur din. Hakan na nuna dokar ba ainahin inda ya cancanci ta yi aiki take yi ba. Nan inda ake tsaurara ta, to ma na wani lokaci ne, Kuma a fahintarmu da manufar samun kudi ne, kurrum.
Shawara, Dukkanin dan kasa nagari dole ya so kasarsa ta zauna Lafiya tare da samun cigaba mai Dorewa. Dole ya yi kishin rayukkan 'yan uwansa da ake kisa ba dare ba Rana tare da salwartar masu da dukiyoyi da aikata albasha kan matansu. Dan haka muna amfani da wannan damar mu yi kira ga al'ummar jahar Zamfara da mu tashi tsaye wajen rokon Allah ya kawo muna zaman Lafiya. Dawwamamme. Tare da kokarin bayar da gudunmawarmu wajen samar da Tsaro a jahar Zamfara da Najeriya baki daya. Dole ne, mu baiwa jajirtattun jami'an Tsaronmu goyon baya.
Sai kuma ita kanta Gwamnati da ta sani wallahi wadannan jami'an Tsaron da aka kawo muna ba su iya maganin matsalar Tsaron jahar Zamfara, su kurrum. Domin karanci da kuma rashin kayan aikin da ya dace da su. Domin dazukkan jahar Zamfara fadi gare su, Kuma ko ina akwai wadannan bata garin. Dan haka in an fatatake su nan yau, gobe can za su bulla, inda babu jami'an Tsaron. Dan haka dole Gwamnatin tarayya ta Karo jami'an tsaron, tare da ba su tallafin da Duk su ke bukata na ganin an magance wannan matsalar.
Daga karshe ina amfani da wannan damar wajen rokon Allah ya taimaki jami'an tsaronmu, ya rika masu, ya ba su nasara a kokarinsu na fatattakar bata gari. Allah ka kawo muna zaman Lafiya Mai Dorewa a jahar Zamfara da Najeriya baki daya.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau (Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Muryar Talaka Ta Kasa Reshen Jahar Zamfara) 08069807496

