GWAMNATIN ZAMFARA A BAYA, BA SU YARDA AKWAI RASHIN TSARO A JAHAR BA, YANZU SUN YARDA WANE MATAKI SUKA DAUKA A ZAHIRI? - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Sunday, 29 July 2018

GWAMNATIN ZAMFARA A BAYA, BA SU YARDA AKWAI RASHIN TSARO A JAHAR BA, YANZU SUN YARDA WANE MATAKI SUKA DAUKA A ZAHIRI?



A shekarun baya gwamnatin jahar Zamfara, kwata-kwata bata yarda akwai wani abu wai shi tashin hankali ba, da ke addabar al'ummar jahar musamman 'yan uwa daga karkara, ba. Duk da mummunan kisan kiyashin da aka shekara kusan bakwai ana yi masu.

Hasalima gwamna mai ci a yanzu, abunda kullum ya ke shedawa duniya shi ne, abunda ke faruwa jahar Zamfara ba. Ba kisan kiyashi ba ne,  fadan manoma ne, da makiyaya.

Wanda hakan ne, ya zama silar, yiwa matsalar rikon sakainar kashi daga ita Gwamnatin jahar. Wanda zuwa yanzu ake cigaba da daukar rayukkan al'ummar jahar ba dare ba Rana. Domin na tabbatar halin da al'ummarmu su ke ciki a karkara rashin katabus ne, muraran da mahukuntan jahar, ke yi.

Domin duk minahikin mataki da za ka ji sun dauka, in ka auna shi da kyau zaka tarar ya zama rufin kan uwar dadi ne, kurrum. Domin akan ce an motsa amma a baka, yayin da a ainahin matsalar ba a ma Kama hanyar magance ce matsalar ba. Uwa uba ta matakan su yi tasiri.

Idan muka dubi matakai uku da Gwamnatin jahar ta dauka wanda shi mu ke gani a zahirance. Wato rufe Dukkanin tashoshin manyan Garuruwan jahar Zamfara da kuma Sanya dokar takaita hawa babura daga karfe takwas zuwa karfe bakwai a 2016 wanda bayan dokar ta yi sanyi aka kara mata tsauyi a ranar 9-7-2018 ta dawo karfe shida na Marece zuwa bakwai na safe.

Dukkanin wadannan matakai Hakika mu muna ganin kawai an Sanya su ne, kurrum amma maganar gaskiya an bar dukan jaki an koma dukan taiki ne. Domin ainahin inda matsalar take ba su ma San da wannan dokar ba. Hasalima babu jami'in Tsaro daya da aka kawo masu. Wanda hakan ya sa yan ta'addar ke cigaba da cin karensu babu babbaka. Wanda na tabbatar dokar ma kara ingiza wannan matsalar za ta yi domin a cikin garuruwanmu rashin aikin yi, na cigaba da yiwa Matasanmu katutu. Hakan na nufin an yi baya ba zane kenan.

To Alhamdulillahi yanzu, kamar yadda mu ka ji a kafar watsa Labarai ta BBC HAUSA cewa ita da kanta Gwamnatin ta aminta da akwai matsalar rashin Tsaro a jahar, Wanda har mu ka jiyo mai taimakawa gwamnan a bangaren watsa Labarai na musamman Malam Ibrahim Dosara na cewa; "A kananan  Hukumomin ZURMI da MARADUN kurrum akwai 'yan gudun hijira sama da dubu goma sha takwas (18,000). Haka akwai Kayukka goma sha takwas da dukkanin mutanen yankin sun yi hijira".  Wannan kenan

Na tabbatar da Duk wani mai bibiyar al'amurran yau da kullum na jahar Zamfara, musamman masu shiga Kauyukan jahar Zamfara, zai ce tabbas akwai matukar ragi a wannan alkalumma na Hon. Dosara. Sai dai kurrum ya fada ne, da ka.

To yanzu in har a kananan hukumomin biyu an samu wadannan adadin mutane, ina ga kananan hukumomin irin Gusau, Tsafe, Bungudu, Mafara, Anka da Maru inda abun ya fi muni?

Mutun nawa yanzu ke gudun hijira? Kauye nawa ya tarwatse?
Wane mataki ita Gwamnatin jahar da ta tarayya suka dauka domin tallafa masu?

Dama masu ilimi sun ce, fahintar Tambaya rabin amsa, ne. Dan haka tunda dai yanzu gwamnatin jahar Zamfara ta yarda akwai matsalar tsaro har al'ummar Dubbai na cikin tashin hankali na rashin rayukka da dukiyoyi. To ya kamata gwamnatin jahar Zamfara karkashin jagorancin gwamna Abdul'azizu Abubakar Yari Mafara. Da ya maida hankalinsa waje daya, ya dawo jaharsa ta ya zauna ya fuskanci wannan matsalar, Dan tabbatar da cewa an kawo karshen matsalar. Ganin abubuwa ne, da dama suka taru suka haifar da ita, amma rashin nuna halin ko in Kula ya sa ana ta kisan gilla ga al'ummarmu. Wanda yanzu haka ma gwamman yana baya kasar, kwata-kwata.

Domin muddun ba a tsaya aka kalli wannan matsalar ba, ba ranar da za a magance ce, ta. Dan haka muna kira ga mai girma gwamna da ya yi wa girman Allah ya dena yawace-yawacen banzar da yake yi, ya dawo ya rungumi mutanensa ko ma samu sa'ida.

Daga karshe muna rokon Allah ya kawo muna zaman Lafiya Mai Dorewa a jahar Zamfara da Najeriya baki daya.

Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau. (Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Muryar Talaka Ta Kasa Reshen Jahar Zamfara) 08069807196

29-7-2018

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here