A yanzu da mu ke cikin mulkin dimokaradiya, ya zama wajibi ga Kowane dan Najeriya, da ke so a zabe shi a wani mukamin siyasa, ya zama yana da jam'iya wadda ta yi rigista da Hukumar zaben Najeriya (INEC). Wanda karkashin jama'iyar ne, Dan Takara zai iya fitowa Takarar kowace kujera. Haka a karkashin jam'iyar ne, mutane za su iya zaben wanda su ke so ya wakilce su ko jagorantarsu. In ko haka ne, jam'iya ita ce ginshikin dimokaradiya.
Saboda haka akwai wasu hanyoyi na tsayar da 'yan takara a Kowane jam'iya. Ya danganta da jam'iyar da mutun ya shiga, domin kowace jam'iya tana da tata hanyar zabar wadanda su ke yi mata Takara.
Ganin haka ya sa na ga ya dace in yi wannan rubutun akan yadda ake zabe a jam'iyar APC a jahar Zamfara.
Jam'iyar APC dai tana da hanyoyi uku na zaben wanda zai yi mata Takara. Kamar haka;
1- Yin Maslaha tsakanin 'yan takara (consensus).
2- Zabe ta hanyar wakilai (delegates).
3- zaben YAR-TIKE.
Dukkanin wadannan zabukkan mun saba ganinsu a jahar Zamfara, in an debe na ukun su. Wato zaben YAR-TIKE. Wanda ba a taba yinsa ba a jahar Zamfara. Tun kirkirar jahar a 1996. Wanda kuma hakan ya sa mutane ba su san yadda ake yinsa ba. Dan haka na ga ya dace in yi wannan rubutun Dan wayarwa mutane kansu.
Zaben YAR-TIKE dai zabe ne, da Kowane mutun mai Shedar zama Dan jam'iyar APC ke da damar yi,
Domin zama da jama'a Apc kuma za ka iya zuwa Kowane cafe a cike maka wani tikitin bayananka tare da baka Shedar zama Dan jam'iyar. Da ka yi haka to Shike nan ka zama halattacen Dan jam'iyar APC, Wanda za ka iya jefa kuri'arka ga Dan Takarar da ka ke so ya yi takara a Jam'iyar APC a babban zaben 2019.
Ana zaben YAR-TIKE a Dukkanin mazabun Dan Takara, misali.
Duk al'ummar Gundumar Galadima GUSAU, za su yi nasu zabe a DAN TURAI PRIMARY GUSAU.
Haka zalika al'ummar mayana, za su yi na su zaben a TOWNSHIP SPECIAL MODEL PRIMARY SCHOOL, GUSAU.
Haka abun ya ke a duk sauran mazabun da mu ke da su. Abunda da dai ake son mutun ya yi shi ne, ranar zaben da zai gudana ka zo da katin shedarka, ka bi layi bayan hoton Dan Takarar da ka ke Goyawa baya. Jami'an da aka dorawa nauyin shirya zaben za su kirga na Kowane bangare, domin fitar da wanda ya yi nasara.
A KULA: zaben da ya gudana a yau, 28-9-2018 akwai labarin da ke shigo muna cewa an hana wadanda suka yi rigista zaben Shugaban Kasa, a yanar gizo zabe. To Hakaki da wata manufa aka yi haka, domin hakan zaben gwamna da ke tafe ku fito kwanku da kwarkwatarku domin neman yancinku.
Allah muna rokonka ka sa mu dace, ka zaba muna shuwagabanni adilai. Ka zaunar da mu Lafiya.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau
28-9-2019

