TASHIN HANKALI KULLUM KARUWA YA KE YI A CIKIN GARIN GUSAU - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Wednesday, 19 September 2018

TASHIN HANKALI KULLUM KARUWA YA KE YI A CIKIN GARIN GUSAU


Hakika halin da al'ummarmu su ke ciki a halin yanzu ya yi muni matukar gaske!

A 'yan shekarun baya, akwai karancin rashin zaman lafiya, a cikin garin Gusau. Sai dai a 'yan shekarun nan abun ya yi munin gaske, har an wayi gari 'yan ta'adda na yawatawa a cikin gari, su yi abunda suka ga dama ba tare da Ance masu kanzil, ba. Assalima Sai bayan sun Kammala aika-aikarsu ne, za ka ga jami'an tsaro sun zo suna kamun kan mai uwa da Wabi wanda bai hana gobe 'yan ta'addar su dawo, dan ba su ake kamawa ba!

Al'ummar garin GUSAU. Muna ji muna gani masifa na tunkararmu. Ba yadda za mu yi!

Yanzu haka, Labarin da ke zo mini 'yan ta'adda fiye da talatin sun afka Birnin ruwa har zuwa kan Wurin Sarki. Dama dai an tabbatar mini da tashin hankali duk Jumu'a Sai ya auku a zawuyya. Ba yadda 'yan unguwar suka iya!

Maganar mutun ya yi yawo da wayar salula a Gusau yanzu ya zama Tarihi, domin kullum cikin farautar mutane ake akan hakan.

Yau din nan ina fitowa gida wanda ya Fara tare ni koken da ya ke yi mini jiya 'yan ta'addar suka tare shi a GRA suka karbe masa waya da kudin da ya ke dauke da su.

Kuma fa Duk wannan aika-aikar abukkanmu NE, kannenmu da suka rasa makoma a rayuwa ke yinta. Mun sani, kuma suna Tare Da mu. Wani lokacin abincin ci, ma wahala ya ke masu, Wanda gajin hakuri ya Kai su ga haka.

ME YA KAWO HAKAN!

Da farko dai zan dora kashi tamanin  da biyar na wannan zuwa ga jagororinnu na Jahar Zamfara, dama dai muna sane da ba mu ne, gabansu ba, sun Kashe bangaren ilimi domin ba wani taimako da ake yiwa 'ya'yan talakawa na su zurfafa karatunsu. Haka zalika bangaren kasuwanci ya samu mummunan koma baya, Wanda kuma jagororin ne sila. Hanyoyin Koyawa Matasa Sana'o'in hannu tuni an Rufe su, ba a bude wasu ba.

Bangaren Numa an Kashe shi uwa uba aikin gwamnati. Wannan ya sa yanzu matashi, a Zamfara in dai ba jahar ya Bari ba, kalilan ne, Daga cikinmu mu ka yaki jahilci.

Haka zalika Kadan daga cikin masu hannu da shuninmu ne, ke taimakawa 'ya'yan talakawa su yi Karatu uwa uba nema masu mafita.

INA MAFITA.

Dole Gwamnatin jahar Zamfara ta kallo talakawan jahar zamfara, ta hanyar bin hanyoyin da za Duk suka cancanta domin dawowa da mu Matasa kan turba ta gari. Haka zalika dole masu hannu da shuninmu su bayar da tasu gudunmawa.

Mu Kuma matasa, mu zama jajirtattun gaske, ta hanyar neman halat duk inda ya shiga.

Ya Allah muna rokonka ka arzurtamu da rabauta duniya da lahira, ka ba mu shuwagabanni masu kirki da kullum za su yi tunanen hanyar tsamo mu daga wannan halin da mu ke ciki. Tare da kawar muna da 'yan jari Hujja ba kullum, matayensu da 'ya'yayensu ne a gabansu tare da yawon banza a kasashen ketare.

Allahumma amin.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

20-9-2018

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here