Duk wanda ya ga yadda talakawan jahar zamfara, suka yi ta nuna bijerewarsu ga yunkurin gwamna Abdul'azizu Abubakar Yari Mafara. Na tsayar da Wanda ya ga dama. A matsayin wanda zai gaje shi, tare da cilastawa wadanda ya ke da fada a gunsu na dole sai sun bi zabinsa. Irin yadda talakawan Zamfara, suka nuna rashin amincewarsu da Wanda ake son ya jagorance su.
Wanda har ta Kai, an Fara Kora tare da tsige duk wanda bai yi biyayya ga wanda gwamnatin ke so ba.
To zai tabbatar da cewa akwai Gagarumar matsala, da za ta biyo baya cikin jam'iyar APC jahar Zamfara. Muddun suka tsaya akan bakansu na cewa al'umma ba su da ikon zaben wanda zai yi takara a jam'iyar. Wanda daga karshe abunda zai kasance shi ne, al'umma za su bar jam'iyar ne. Domin zaben gwaninsu. Ko a wace jam'iya ya fito!
Na tabbatar duk jam'iya na bukatar al'umma NE, idan mutun daya zai Barta ba za ta so ba. To wallahi muddun aka ce KOGUNA ne, zai zama Dan Takarar gwamnan APC na jahar Zamfara. To Duk abunda ya biyo baya....
Dan haka ya kamata jagororin Apc na kasa, so tabbatar da cewa an tsayar da Dan Takara mai nagarta da zai iya kawo jahar Zamfara.
Kukan kurciyar nawa kenan!
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau
17-9-2018

