DUK BAZAMFAREN KIRKI DOLE YA KYAMATA, TARE DA YAKAR YUNKURIN SHEHI, NA TSAYAR DA KOGUNA, A MATSAYIN MAGAJINSA! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Saturday, 15 September 2018

DUK BAZAMFAREN KIRKI DOLE YA KYAMATA, TARE DA YAKAR YUNKURIN SHEHI, NA TSAYAR DA KOGUNA, A MATSAYIN MAGAJINSA!

DUK BAZAMFAREN KIRKI DOLE YA KYAMATA, TARE DA YAKAR YUNKURIN SHEHI, NA TSAYAR DA KOGUNA, A MATSAYIN MAGAJINSA!

Gwamna Abdul'azizu Abubakar Yari Mafara, shi ne gwamna na 3 a jerin gwamnonin da su mulki jahar Zamfara a mulkin farar hula in mun debe gwamna na farko na mulkin soja.

Kafin shi, mun yi Sanata Ahmad sani(Yariman Bakura) wanda ya yi shekaru takwas yana mulki, Wanda a lokacin lokacin mulkinsa ne, jahar Zamfara ta yi suna a bangaren addini, duk da wasu na ganin da sunan siyasa ya jaddada ta, ko dai da mene ne, Allah dai ya san abunda ke zuciyar bawa Kuma zarihi Dan Adam ya kamata ya duba. Akasinsa ya barwa Allah ta'ala domin shi ne masanin abunda ke boye. Amma dai zan iya cewa ko da mene Alhamdulillahi mu matasa Shari'ar ta yi tasiri a rayuwarmu har zuwa yau jahar Zamfara akwai karancin aikata badala a bayyane. Wannan kenan!

Bayan ya sauka Mataimakinsa Mamuda Aliyu Shinkafi ya gade sa, ba a dauki dogon lokaci ba, suka raba jaha da Tsohon mai gidan nasa (Sanata Ahmad Sani) shima dai ya yi iya nasa kokari Alhamdulillahi ba za mu iya fallasa Gwamnatinsa da wani aikin assha ba, in ka debe halinsa na saku-saku da al'amurra da sanyin hali da ya sa makarabansa su ka yi yadda su ka so da dukiyar talakawan jahar. Wanda hakan ne, ya cilastawa Zamfarawa neman canji Ido rufe.

Bayan mun yi nasarar kawar da gwamnatin Mas a 2011 mun zabi gwamna mai ci a yanzu wato gwamna Abdul'azizu Abubakar Yari Mafara. Da zummar zai kawar muna da miyagun shingayen da makaraban gwamna Mas ya daddasa muna kan hanya tare da  kawar muna da miyagun doddanin da suka zagaye Gwamnati suna wandakarsu da dukiyarmu.

Alhamdulillahi gwamnatin Shehi ta yi nasarar kawar da duk wani dan ba ni na iya. Hasalima gwamna ya zama Jarumin da ya iya tafiyar da komi da kansa babu wanda a dan gaban goshinsa in ka debe mutun biyu sai Kuma 'yan garinsu. Wanda ko su biyun ta su ce ta zo daya.

Duk wani bazamfare dama wajen zamfara zai yabawa Shehi akan Abu daya da Alhamdulillahi a jahar Zamfara ba a taba samun gwamna da ya yi wa Zamfarawa shi, kamar gwamna Shehi ba. Wato tituna, shakka babu Shehi ya yi tituna a birni da kauyen jahar Zamfara.

Sai dai, Kash! In ka Debe wannan bangaren ba wani bangare da za ka yaba masa ko ka ba shi maki 35 cikin 100. Hasalima, ya tafiyar da mulkinsa a hangunce ce. Tare da tarwatsa Zamfarawa ta kowace sabga. 

Idan muka dubi bangaren, ma'aikata, 'yan kasuwa, ilimi, kiyon Lafiya, walwala,almubazaranci da dukiyar talakawan jahar, dama wasosonta da ya yi, Sai kuma yawace-yawacen banzar da ba su da amfani da gwamnan ya yi ta yi a lokacin mulkinsa da uwa uba rashin Tsaro da yanzu ba wata jaha a Najeriya da ta kai jahar Zamfara fuskantar matsalar. Wanda kuma kacokan muna ganin cewa akwai sakacin gwamnatin jahar Zamfara cikin wannan aika-aikar. Ganin yadda gwamnatin ta yi ta nuna halin ko-in-kula akan matsalar.

To Alhamdulillahi yanzu lokacin sauyin gwamnati ya zo, dudu saura watanni ya sauka. Dan haka ya tabbatar akwai barazana babba a tare da shi.

Domin na farko dai dole zai fuskanci kalubale ga duk gwamman da zai gaje shi, Musamman idan gwamnan ya yi wa mutanen Zamfara abun kirki za a gano tabbas Shehi ya yi aika-aika, haka zalika za a iya fallasa aika-aikar da ya yi, har tunon asiri ya shigo na wasoson dukiyar talakawan Zamfara da ya yi, Wanda karshe, EFCC da ICPC ba za su zura mashi Ido ba. 

wanda duk Bazamfaren kirki yanzu fatansa sauyi daga wahalhalu da kunci da aka sha, tare da samun shugaba wanda zai yi jagorance mu domin magance matsalolin da mu ke fama da su. Sai dai kash! Shi ba haka abun ya ke a bangarensa ba. Hasalima gurinsa shi ne mu dawwama cikin wannan halin da ya yi sanadiyar jefa mu. Wanda hakan ma ne ya dauko wanda bai Kai shi nagarta ba, dan zuwa gaba mu ce gwamma Shehin da wannan.

Dan haka Sai ya yi kokarin ya samo wanda na farko dai duk aika-aikar da yi a lokacin mulkinsa, to shi ne Dan gaban goshi, domin da shi aka yi, Hasalima shi ne, ya zamar masa kwamishin kudi na shekaru hudu wanda duk wata aika-aikar da ya yi da shi ya yi ta. Wanda ya tabbatar zai rufa masa asiri. Wato Hon. Mukthar Shehu Idris (Kogunan Gusau) 

Haka zalika mutunen da ya tabbatar da wajen yawace-yawacen banza,  shafe shi, domin shi kwata-kwata ko a mahaifarsa (GUSAU) bai da gida haka zalika yana iya sama da watanni biyar bai shiga ma'aikatar da ya ke zama kwamishina cikinta ba. Halima jahar Zamfara bai iya Mako daya cikinta. Maganar shiga shirgin al'umma na daurin Aure ta'aziya, ko jaje in wata musiba ta samu al'umma ba ya zuwa balantana ya rabi Talaka ko ya San halin da mu talakawa mu ke ciki. Hasalima ni, ban taba ji ko ganinsa wajen ko dayan wadannan ba.

Mutun wanda kwata-kwata bai da wani sahihin Tarihin na aikata alheri ga al'ummar jahar Zamfara.

Wanda ya tabbatar da in ya zama gwamna bangaren dukiyarmu da suka raruma ta zama tarihi, haka zalika aibun da wannan zai yi wa talakawan Zamfara sai ya fi nasa. Dan haka za a manta da nasa kwata-kwata.

Hujja a nan ita ce, kamar yadda ya fada cewa, "an fitar da Dan Takarar gwamna daga yankin Zamfara ta Tsakiya ne, domin Tun Kafuwar. Mulkin dimokaradiya dan yankin bai taba zama gwamna ba."

Sai dai abunda har yanzu munka kasa fahinta shi ne, a yankin yanzu haka akwai 'yan Takarar gwamna a APC kurrum biyar hudu Duk 'yan Gusau. Abun tambayar a nan shi ne. Me ya sa duk da sai dukkaninsu sun fi fitar su a fili na son kujerar Kuma a zahirance sun fi shi gogewa a siyasa, da kuma yiwa al'ummar Zamfara ayukkan kirki a mukamai daban-daban da suka rika. Bai sa gwamman ya dauki cikinsu ba? 

Wanda hakan ya tabbatar muna ceto ba gurinsa a samu cigaba mai Dorewa a jahar Zamfara ba. 

Dan haka muna amfani da wannan damar mu yi kira ga uwar jam'iyar APC ta Kasa da ta yi duk mai yuyuwa na tabbatar da cewa Wanda al'umma su ke so, ne. Ta tsayar Dan Takararta na gwamnan jahar Zamfara. In Kuma ba haka ba, wallahi jam'iya ba, addini ba ce, a 2019 cancanta za mu bi ba wai son zuciya ba.

Haka zalika muna amfani da wannan damar mu yi kira ga al'ummar jahar Zamfara, da mu sani cewa tun tarihinmu ba a taba yi muna doki Dora ba, Kuma a 2019 ba za a soma ba. Dan haka, in har uwar jam'iyar APC ta tsayar da Wanda ba mu kauna. To mu hada kanmu mu kayar da shi, ta hanyar zaben wanda ya fi shi alheri gare mu. Ko wace jam'iya ya fito, domin jam'iya ba addini ba ce da za a ce ba a canza shi.

Allah muna rokonka ka arzurtamu da Shugaba adili wanda ceto rayukkanmu daga kisan dauki dai-dai da ake yi muna. Ya Allah ka kawo muna Shugaba wanda ke kaunarmu da gaskiya tare da kokarin Dora al'ummar jahar Zamfara kan turba ta gari, ba hanyar bata da kauce maka ba, ya Allah.

Allahumma. Amin

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau

15-9-2018

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here