Ganin halin da al'ummar jahar Zamfara mu ke ciki yanzu.
Da dama daga cikin al'ummar jahar yanzu haka, sun Kaura dan ceton rayukka da dukiyoyinsu, mu da mu ke zaune cikin jahar kullum Hankalinmu tashe ya ke, yayin da al'ummar karkara ke kwana zaune ko saman ita ce Dan ceton rayukkansu daga mahara. Mu Kuma da ke cikin gari kullum cikin dar-dar da zullumi mu ke yawo a kasa, na shirin yi muna kamshin dan-goma. Saboda kirkirarren rashin aikin yi da aka samarwa Matasanmu, Wanda hakan ne ya sa da dama daga cikinsu zama barayin karfi, da ke kwace waya da kayan amfani ga duk wanda su ka yi Ido biyu da shi a bagire da ke da karancin sawu!
Ma'aikatan Gwamnati da dama daga cikinsu sun zama 'yan mola, domin an rike masu hakkoki Duk wata Darajja ta su ba a gani. Tuni harkar ilimi ta tabarbare wanda ya gadar da Mummunan jahilci ga al'ummar jahar Zamfara. Mu 'yan kasuwa ba maganar mu, domin an Kashe Duk wasu hanyoyi da kasuwancinmu zai bunkasa, Wanda ya sa da dama daga cikinmu sun Kare...
Kadan kenan daga cikin halin da gwamnatin da ke ci yanzu ta jefa al'ummar jaharmu. Wanda Kuma yanzu ta yi uwa ta yi makarbiya dole sai mun zabi wanda take ganin zai Dora daga inda Ta tsaya....
Dan haka al'ummar jahar Zamfara, in dai mun gamsu za mu cigaba da zama halin da mu ke ciki ko ma wanda ya fi shi muni. To za mu iya zaben wanda zai Dora daga inda sunka tsaya.
In Kuma akasin hakan to Sai mu tashi daga barci, kuri'armu 'yancinmu. Da ita za mu iya canzawa tare da dora Wanda ya yi muna ko mu ke da yarda da SHI.
Dan haka ya kamata 'yan uwa mu sani cewa muna fama da bakin talauci, Kuma sun saci kudinmu da za su ba mu dan mu zabe su. Dan haka mu fito kwanmu da kwarkwatarmu, wajen zaben wanda ba su ba. Dan yin jahadin ceto al'ummarmu daga wannan mummun halin da mu ke ciki.
Allah ya ba mu sa'a ya yi muna tsari da zaben 'yan jari Hujja.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
30-9-2018

