MENE NE AMFANIN GWAMNATIN JAHAR ZAMFARA, GA MU MATASAN JAHAR. DA HAR ZA SU NEMI MU YI RA'AYINTA? - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 1 October 2018

MENE NE AMFANIN GWAMNATIN JAHAR ZAMFARA, GA MU MATASAN JAHAR. DA HAR ZA SU NEMI MU YI RA'AYINTA?

Gwamnatin Jahar ZAMFARA da Mai Daraja Gwamna ABDUL'AZIZU ABUBAKAR YARI MAFARA, Ke cigaba da jan zarensa, bayan ya yi Nasarar Jan na farko ba tare da ya tsunke ba.

Tun bayan kafuwar Gwamnatin a ranar 29-5-2011 zuwa yau. Ba ni tunanen akwai wasu gungun matasa da sunka amfana da wannan Gwamnatin, in ka debe wasu gungun matasa da mafiya yawansu sun taso cikin rashi kuma har yanzu su ke cikinsa. Wadanda sunka sadaukar da rayuwarsu wajen kafa gwamnatinsa Tun a 2011, yanzu kuma ya mai da su a cikin kwatocin garin Gusau. Suna cigaba da yasarsu.

Tuni dai duk wata hanya da ake bi a taimaki matasan jahar da mai girma Tsohon Gwamna Alh. Ahmad Sani da wadda magadinsa ya dan dora, tuni wannan Gwamnatin ta kashe su.

Farawa da kashe duk wani bagire na koyar damu sana'o'in hannu domin mu dogara da kanmu. Tare da taimakon iyayenmu da 'yan uwanmu.
Maganar a taimaki rayuwar matasan jahar su nemi ilimi ba a maganarta, domin duk wani dalibin da ya kammala digirin farko NCE ko diploma bai taba amfana da naira da sunan tallafin gwamnatinsa ba. 

Matasan da Gwamnatin ta isko suna kasuwanci tuni ta yi kutunguilar da za ta karya su, ta hanyar Daukar matakai iri daban-daban da zummar murkushe mu  a cewarta wai yunkurin Samar da tsaro. Wanda hakan ya sa da dama daga cikinmu sun yi hijirar dole, mu da munka yi karfin Hali, garin na shirin fin karfin zamanmu.

Idan matashi ya yi karatu a jahar Zamfara, sai dai Ya Kalli Gwamnatin tarayya in yana son aikin Gwamnatin, in kuma Jahar zai kallo! To fa da aiki. Domin tun da Gwamnatin ta hau kan karagar mulkin Jahar bata dauki matashi daya aiki ba. Wanda hakan kansa dole in mun turza mun yi karatun mu cigaba da zurawa takardun idanu, domin ba wajen Kai su!

Babbar masifar ita ce; Wallahi duk wanda Gwamna Shehi zai baiwa jahar a Matsayin Gwamna. Wallahi zai bar masa tarin matsaloli ne da sai ya Kai namijin gaske zai iya daidaita jahar.

Kwatsam! Sai kuma mu ka ji shi da kansa ya dauko wani mutun wanda, Duk wanda ya Sanshi a matsayin da ya rika na shekaru takwas na kwamishina a jahar  zai iya bugun gaba tare da fadin gwamma shi gwamman ta Kowane hauji da shi Wanda ake son Dora muna da karfi.

Wanda a tunanenmu duk wani hali da mu ke ciki, da taimakon wannan Dan tahiliki aka jefa mu ciki, Hasalima shi wannan dan tahaliki shi ne, ja gaba wajen jagorantar dora gwamna ga cigaba da yi muna aika-aikar. Wanda shi gwamnan ya dora wannan Dan tahaliki, ne dan dai ya Rufe aika-aikar shekaru bakwai zuwa takwas din da ya yi, tare da cigaba da jefa rayuwar talakawa cikin Kunci wanda hakan zai sa, a manta da aika-aikar da shi gwamna mai ci a yanzu ya yi.

Dan haka Matasan jahar mu ne ke zabe, Sai mu zabi cigaba ko sauyi nagari.

Allah kai ne, ka halicci mu matasan jahar zamfara, kuma ka kebe wani nau'in na mulkinka ka baiwa wannan bawa naka!

Allah kai ne ka ce mu rokeka, kana karbar addu'ar bayinka. Allah ka karbi addu'armu, ka ceto mu daga cikin wannan mummunan yanayin da mu ke ciki.

Allah mun tuba!

Ya Allah ka albarkaci rayuwarmu ka zaba muna shuwagabanni masu tausayinmu a nan gaba!

Allah duk Shugaban da ba ya tausayinmu, Allah ka sansa, muna rokonka ko kujerar KAMSILA kada ka ba shi. Allahumma amin.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

1-10-2018

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here