Labarin da ke shigo muna Yanzu daga makusantan Marayun nan biyu Hasana da Husaina, sun tabbatar muna da cewa. Barayin da suka sace su, sun nemi a ba su NAIRA MILIYAN 100 kafin sakin 'yan matan.
'Yan matan dai Marayu ne, ba su da uwa ba su da uba.
Haka zalika majiyar ta sheda muna ko Dubu Dari 100k yayansu baya da kasa. Hasalima da dubaru, yayan nasu ya ke yi domin daukar dawainiyarsu, da sauran kannensu.
Hasana da Husainar dai 'ya'yan Marigayi Alhaji bala Dauran Dan Galadiman Dauran ne. An sace su ne cikin daren jiya laraba 24-10-2018 a gidansu da ke Dauran, bayan sun tafi ganin gida a garin Dauran din, daga nan cikin garin Gusau . 'Yan uwan 'yan biyun sun nemi Gwamnati ta taimaka masu domin ceto rayuwar yan matan.

