Yau Laraba 17-10-2018 Shugaban kanfanin Na'alla Motors, Alh. Bashir Namada Ataka (Sarkin Motar Shehi) ya cika alkawarin da ya daukarwa al'ummar Garin Tazame da ke cikin karamar hukumar mulkin Bungudu, na fente masu Masallacin Juma'arsu.
Da ya ke hannunta kayan aikin Wanda suka hada da; Manyan bukitayya 14 na fenti da kananan biyu da kayan fentin ga kwamitin masallacin, Shugaban Kungiyar Matasan zamfara ta tsakiya. Malam Rufai Bala Ub Gusau. Ya bayyana cewa; " kamar yadda kuka sani wannan Dan tahaliki ya daukarwar kansa alkawarin wannan aikin ba dan kun roke shi ba, ranar lahadi bayan ya zo aikin Gyaran makabartarku.
"To Alhamdulillahi mu ne jakadunsa da ya turo da wadannan kaya, kuma ya sheda mani da in tabbatar maku da wani muhimman aiki ne, ya sa bai zo ba. Amma gobe insha Allahu ni zan zo, Kuma za mu biya ma'aikatan da suka yi aikin.
"Kamar yadda kuka sani Ataka ba ma'aikacin Gwamnati ba ne, kuma bai da kowane mukamin siyasa. Dan haka abunda ya ke nema gareku shi ne, addu'a a wajenku na Allah ya yalwata masa wajen kasuwancinsa.
"Daga karshe matashin ya yi Kira ga 'yan uwansa matasa da su zama jakadun alheri."
Da ya ke maida jawabi na'ibin Masalacin Juma'ar, ya nuna jin dadinsa matukar gaske ga wannan aikin tawali'un na Sarkin Mota. Ya yi addu'ar Allah ya biya masa bukatunsa na alheri. Ya yalwata arzikinsa. Daga karshe ya yi Kira ga sauran Al'umma musamman masu hannu da shuninmu da su yi koyi da shi.




