Al'ummar garin Tazame da ke cikin karamar Hukumar Bungudu, sun yabawa gwazon Alh. BASHIR NAMADA ATAKA (Sarkin Motar Shehi). Al'ummar sun yaba masa ne, akan aikin Tawali'unsa.
A cewar babban limamin Garin ta zame, "Hakika ba mu da abunda za mu cewa wannan Dan tahiliki Sai godiya. Domin mu dai ba mu taba ganinsa da Ido ba, Sai dai Labarin ayukkan alherinsa. mu dai kurrum munga sun tsaya Sallah, bayan mun Kammala muka bayar da Sanarwar aikin gyaran makabarta.
"Ba su ce muna Kala, ba. Haka mu ma haka dan ba mu san shi ba, kawai washe gari muka ga ya kwaso tawagarsa dauke da Abinci da abun sha, cewa shi ma ya zo aikin Allah.
"Hakika mun ji dadi da zuwansa, musamman zuwansa ya karfafa muna Kuma ya Karawa Matasanmu kwazo, uwa uba ga Kyauta da ya yi muna kuma ya yi muna alkawarin fente muna masallacin Jumu'a dinmu, Hakaki muna godiya, Allah ya saka masa alheri."
Da ya ke jawabi a wajen gyaran makabartar Sarkin Motar Shehi, ya bayyana cewa; "aikin gyaran makabarta, Abu ne muhimmi a rayuwa, domin wadanda ke Raye ke yinsa, Kuma makabarta gidan kowa ce, Dan haka ya zama wajibi Duk mutun mai tunane ya gyara gidansa kafin lokacin shiga.
"Dan haka, ma ne ya sa na ga ya zama cilas in shiga cikin wannan aikin domin gyaran gobe na. Kuma Insha Allahu zan fente Masu masallacinsu na juma'a ko robar fenti nawa zai ci. Domin masallaci dakin Allah ne, kuma duk wanda ya gyara, Allah zai taimake shi. Dan haka na ke rokon Allah ya sa wannan aikin ya Kai ga Mizanin ayukkan alherina."




