MATASA SUN YI GANGAMIN KIRA GA 'YAN SIYASAR ZAMFARA DA SU YI SIYASA BA DA GABA BA. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 15 October 2018

MATASA SUN YI GANGAMIN KIRA GA 'YAN SIYASAR ZAMFARA DA SU YI SIYASA BA DA GABA BA.


Ganin yadda aka samu rasa rayukka da dukiyoyi a zaben fitar da gwani kurrum a jahar Zamfara, ya saka gamayyar, kungiyoyin da suka hada da;

Kungiyoyin matasa 
Kungiyoyin Dalibbai 
Kungiyoyin Kare hakkin Dan 
Kungiyoyin 'Yan kasuwa 
Kungiyoyin Kabilu 
Kungiyoyin Addinai.
Kungiyoyin Mata da sauransu, karkakashin kungiyar Labour Room Global initiative. 

Suka shirya gangami inda suka yi kira ga yan siyasa da sauran al'ummar jahar Zamfara da a yi siyasa ba da gaba ba. 

A lokacin gangamin dai  daya shafi Dukkanin bangarorin al'ummar jahar Zamfara, da Dukkanin mazauna jahar, za an mika Kasidu da ke dauke da sakonnin muhimmancin zaman Lafiya tare da Illar rashin Lafiya. Tare da Gabatar da jawabai ga manema Labarai a akan nisantar kai ga Siyasar zubar da jini da rungumar akasinta.

Taron dai ya gudana ne yau Litinin  15-10-2018 wanda aka Fara da Misalin karfe: 8:00 na safe. Wanda aka fara bakin Sambo Sikandire, mu biyo ta shataletalen Central Police Station aka zarce  Daga nan aka bi shataletalen Bello Bara'u daga nan  biyo ta kasuwar dare aka wuce gidan Sarki daga nan a Gabatar da jawabai ga manema Labarai

A lokacin da ya ke jawabi a fadar Sarkin Katsinan Gusau, Shugaban kungiyar da ta shirya gangamin Amb. Nura Isah Gusau, ya bayyana cewa kungiyar labour room ta yi wannan hubbasar ce, ganin yadda ake ta samun Kashe-Kashe, da hasarar dukiyoyi da sunan siyasa. Inda ya yi kira ga 'yan Siyasar Zamfara da su rungumi siyasa mai tsabta tare da kauce Duk da wani yankuri na siyasar zubar da jini.

Da ya ke maida jawabi, Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau Alh. Ibrahim Bello Gusau. Ya nuna jin dadinsa Matuka da yunkurin wannan kungiyar, ya kuma yi kira ga sauran kungiyoyin jahar Zamfara da su yi Koyi da kungiyar. Haka zalika ya yi kira ga yan siyasar Zamfara da su rungumi siyasar lumana. Daga karshe ya yi kira ga Matasan da suka halarci zanga-zangar da su zama jakadu nagari, wajen Kira ga 'yan uwansu da Kada su taba Sanya kansu ga sha'anin tada zaune tsaye.

Rubutawar: Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau 
SSA ON MEDIA AND PUBLICITY, To the labour room Governor.

15-10-2018


Post Bottom Ad

Responsive Ads Here