BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA GWAMNAN JAHAR ZAMFARA, AKAN DAUKAR NAUYIN YIWA SHUGABAN APC NA KASA BORE. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Friday, 26 October 2018

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA GWAMNAN JAHAR ZAMFARA, AKAN DAUKAR NAUYIN YIWA SHUGABAN APC NA KASA BORE.

Tare da fatan kana cikin koshin lafiya, Mai girma gwamna na, na nemi in rubuta maka wannan wasika a wannan kafar Domin nan ne kurrum kafar da na ke da tabbacin wasikar za ta riskeka. Ko makusantanka, da na tabbatar za su sheda maka.

Mai girma gwamna, ba na rubuta maka wannan wasikar Dan goyon bayan, Shugaban jam'iyarku ta APC na kasa Comrade Aliyu Adams Oshiomole, ba. Ko ma jam'iyar ita kanta ba. A'a na rubuta maka wannan wasikar ne, domin nuna rashin jin dadina da nuna rashin halin Ko in kula da Kake cigaba da yi muna. Ka mayar da hankalinka a sha'anin jam'iyar Ko ince Wanda Kake maitar ya gaje ka.  Wanda a tunanen Yanzu ba irinka ne, ya dace a ce kana da Lokacin da za ka shirya zanga-zanga nuna bacin rai ga wani abunda daban ba da ya fi rayukkan al'ummarka da dukiyoyin talakawanka, da a kullum ake dauka ba. Hasalima ina hasashen duk Wanda zai baka shawarar rungumar zanga-zangar wata jam'iya cen, to ba masoyinka ne, da Zamfara Baki daya ba.

Duk da cewa Mai girma gwamna, ka sani duk wani rashin jin dadin da Kake nuna wa da  rashin makoma da jam'iyar APC ta jahar Zamfara ta ke ciki. Kai ka jefa jam'iyar ciki koma ka ke cigaba da jefa ta ciki. Wanda bayan amfani da karfin mulkin da ka so ka yi yaki tasiri wajen dora Wanda Kake so, Yanzu kuma ka koma kame-kame Wanda da farko dai ka shirya Zabe, Wanda a tunanenka fadar Shugaban kasa da uwar jam'iya za su  karba, amma suka juya baya. ka nufi kotu Wanda hasashenmu lauyoyi da masana Shari'a ne kurrum za su ja rabonsu, tare da tarin ilimi da hakan zai barwa sashen shari'ar Najeriya. Yanzu kuma ka dauko hayar mutane daga kananan hukumomi da kauyukka, ka ba su kudade su nuna ba su kaunar mulkin Adam Oshiomole, Wanda na tabbatar su kansu wadanda ka tara din, ba su san su takammen su waye ba, saboda tsabar jahilci da talaucin da kuka kirkira muna, Wanda ya sa suka kasa yin tataccen tunane, gano illar da gwambatinka ta yi masu. Wannan kenan!

Abun mamaki ma, gwamna irin na Zamfara Wanda Allah ya yi gatan duniya, ya yi shekaru bakwai, ya harari na takwas a matsayin gwamna kuma Gwamnan gwamnonin Najeriya. Madadin ya godewa Allah ta hanyar barinsa ya yi nasa iko kamar yadda shi ne ya kawo shi a matsayin Gwamnan jahar Zamfara.

Wanda kamata ya yi ya maida hankali a watanni bakwai dinda suka rage maka ka yi tsayen daga, Sai ka tabbatar da an dena kisanmu  al'ummarka da satarmu da salwantar muna da dukiyoyin da ake yi kullum daren Allah ta'ala. Amma ina ka himmatu wajen tsayar da Wanda ka ke so dole shi zai gajeka.

Ina ganin kamar bai ma canci hankalin Bazamfare ya tafi ga wata tatubar siyasa a wata jam'iya cen ita ba, domin ita da rashinta duk sai Zamfara ta yi gwamna a 2019.

Dan haka, muna amfani da wannan damar mu yi Kira gareka da ka debe hannunka a cikin sha'anin neman mulkin jahar Zamfara tunda Kai dai ka yi naka lokacin Ko mu ce kana Kai, ka maida hankali wajen yi muna aikin da muka Zabe ka dan ka yi muna.

Domin wallahi tallahi halin rashin tsaron da ya haifar da tsoro na ban mamaki da ya yi wa mu talakawan jahar Zamfara yawa, ya yi muni matukar gaske. Kullum Cikin satarmu da kisanmu ake yi tare da salwantar muna da dukiyoyinmu a kauyukka. Mazauna cikin manyan garuruwan jahar Zamfara, muna fama da tada zaune tsaye daga matasan da aka shekara bakwai ana Tarawa ba, aikin yi, ba karatu ba makoma ta gari, kullum sai sace-sace da daba da aikin masha'a.

Daga karshe muna rokon Allah ya sa wannan kiran ya kai ga kunnuwan wadanda munka yi ta domin su. Ya kuma ba su ikon share muna hawayenmu.

Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

26-10-2018

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here