A rayuwa, akwai wasu al’amurra da lokaci ne kawai ke magance su. Wannan matsalar tana daya daga cikinsu. A duk lokacin da Shugaba Buhari yayi yunkurin barrantar da kanshi akan wannan matsalar, sai yunkurin ya haifar da karin rashin yarda, da zumudi da kokwanto na rashin amincewa da cewar lallai Shugaban ya mallaki wannan takardar shaidar kammala sakandare.
Da ace nine Shugaba Buhari, ba zanyi yunkurin barrantar da kaina ba ko kadan. Zanyi biris da al’amarin. Duk wanda bai gamsu da shiru dina ba, shi zaije kotu ya tabbatar ma duniya cewa ban cancanci in tsaya takarar Shugaban Kasa ba.
Idan zancen ya kai kotu, za’a dogara da Sashe na 131 na Kundin Tsarin Mulki na Nigeria (1999 kamar yadda akayi mishi gyaran fuska), wanda yace: babu wanda zai cancanci tsayawa takarar shugabancin Nigeria sai haifaffen dan kasan Nigeria; kuma ya haura shekaru arba’in da haihuwa; kuma dan wata jam’iyyar siyasa ce sannan kuma ita jam’iyyar ta dauki dawainiyar zaben sa; kuma na karshe, ya zama yayi karatu har matakin a kalla takardar shaidar sakandare ko makamanciyar ta.
A bangare daya kuma, Sashe na 318 na Kundin Tsarin Mulki na Nigeria, ya fassara abunda ake nufi da takardar shaidar kammala sakandare ko makamanciyar ta cewa tana nufin:
a- Shaidar kammala karatun sakandare ko makamanciyar ta, ko Grade II, ko takardar shaidar City and Guilds; ko
b- Karatu wanda yakai matakin shaidar kammala sakandare; ko
c- Shaidar kammala Aji Shidda a Primary ko makamanciyar ta, hadi da:
i. Aikin gwamnati ko ma’aikata mai zaman kanta a cikin Nigeria na tsawon akalla shekara goma, a kowane mataki muddin hukumar zabe ta kasa (INEC) ta gamsu dashi;
ii. Hallartar kwasa- kwasai da koyarwa a karkashin wannan ma’aikata na jimillar tsawon a kalla shekara daya daidai da gamsuwar hukumar zabe ta kasa (INEC);
iii. Iya karatu da rubutu da fahimta da kuma bayani a cikin harshen turanci daidai da gamsuwar hukumar zabe ta kasa (INEC); da kuma
d- Kowace irin takardar cancanta da hukumar zabe (INEC) ta yarda da ita.
Dukkan wadannan ka’idodi ba a hade suke ba, la’akari da amfani da akayi da kalmar “ko” in banda ka’ida Mai Lamba C wadda ita kuma hade take da ka’idodin da suke karkashin i, ii da iii.
Masu inkarin cewa Shugaba Buhari bai cancanci ya tsaya zaben shugaban kasar nan ba, a cikin matukar girmamawa garesu, basu fahimci tanadin Sashe na 318 na Kundin Tsarin Mulkin Nigeria ba, domin koda ace Shugaban bai cancanta ba a karkashin Sashe na 131 da Sashe na 318(1)(a)(b) na Kundin Tsarin Mulki, ita Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) tana iya wanke shi a karkashin Sashe na 318(1)(c)(i)(ii)(iii) da (d) na Kundin Tsarin Mulki. Amincewar ka daban, amincewar hukumar zabe daban. Kuma amincewar hukumar zabe a keso, ba taka ba. Wannnan shine matsayar doka a halin yanzu har sai an canza ta.
A ra’ayi na, wannan takaddama bata da wata fa’ida. A wannan lokaci, bai dace Yan Nigeria suna bata lokaci akan abubuwan da basu da wani tasiri a garesu ba bayan kuma akwai muhimman abubuwa da suke damun al’umma: irinsu al’amarin tsaro wanda kusan ya shafi kowace jiha a kasar nan; zaman kashe wando; jahilci; noma;kasuwanci da sauran al’amurran da suka sanya rashin tabbas din goben kasar nan.
A ganina, kamata yayi Yan Nigeria su himmantu wurin auna nasarorin da Shugaba Buhari ya samu a lokacin mulkin sa, sai kuma su auna da alkawullan da yayi masu a lokacin yakin neman zabensa, daga nan ne zasu auna ko ya cancanta su sake zaben sa a matsayin shugaban Nigeria karo na biyu.
Galadi lauya ne mai zaman kanshi a garin Gusau. Shine shugaban Gidauniyar Bello Galadi Foundation kuma shine Shugaban Lauyoyi na Jihar Zamfara.
Za’a iya samunshi a muhammadbel_law@yahoo.com ko muhammadbellaw80@gmail.com
5th November, 2018.

