MAGOYA BAYAN GWAMNAN ZAMFARA, SUN JUYAWA BUHARI BAYA A ZABEN 2019 - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Wednesday, 23 January 2019

MAGOYA BAYAN GWAMNAN ZAMFARA, SUN JUYAWA BUHARI BAYA A ZABEN 2019


Dama masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce; "in ka ga Kare na sunsunar talkami, kar ka ji ko dar dauka zai yi"

A wannin baya, duk Inda ka ga kafar shugaba Buhari to Shehi na rabe da shi kamar alif da lam! A tunanen duk wani bazamfare shi ne yarda ce da aminta da son Allah da annabi Gwamnan ke yiwa Shugaba Muhammadu Buhari, shi ya sa yake matse masa Dan kwasar tubarraki. Sai dai kash! Ashe kamun kafa ya ke nemi, na Shugaban ya ba shi dama ya yi yadda ya so da talakawan jahar Zamfara. Ta hanyar Dora masu Wanda zai juya yadda ya so, tare da taimaka masa wajen Iyar da kashe Zamfarawan kwata-kwata. Sai dai abunda a bai sani ba kar! Dattijon ke kallonsa. Sai da lokacin zaben fitar da gwani, ya zo shugaba Buhari ya ce abar uwar jam'iyar APC ta yi abunda ya dace, I domin su ke da ruwa da tsaki akan tsayar da Dan takara ta yadda zai zama Maslaha ga talakawa waya Allah zaben wakilai, kato-bayan-kato ko sasanci. Wanda daukar matakin yin kato-bayan-kato a Zamfara ya sa, Gwamnan ya kasa Kai bantensa....

Dan haka daga lokacin Gwamnan jahar Zamfara da duk wani Mai yi masa biyayya ja baya ga rabar shugaba Buhari, Wanda yanzu haka duk yakin neman zaben da shugaba Buhari ke yi, wuri daya aka taba nuna Gwamnan yana yake (Kaduna). Wannan kenan!

Wanda masharhanta Manya da kanana irina sun Dade da Gama hasaso cewa; Gwamnan ko dai ya bar APC ko kuma ya yi angulu da kan zabo ta hanyar yiwa jam'iyar Illa tun daga matakin shugaban kasar har zuwa na Gwamna (in an tsayar da Wanda ba zai bi mas'habarsa ba).

To alhamdulillahi jiya Talata 22-1-2019 na yi wani rubutu da na yi hasashen irin matsaloli da turjiyar da shugaba Buhari zai fuskanta a 2019 a jahar Zamfara Inda Na so in sanya irin wannan Maganar a rubutuna na jiya! Sai dai na taba ta sama-sama. Ga shi ta tabbata ko in ce ta Fara tabbata.

Wannan hoto da na dauko dauke da sunan Abubakar S limanchi. Rubutun wani Dan gani kashenin Gwamnatin Shehi ce kuma cikin yaransa da in wuta Shehi ya ce su fada, za su fada. Kamar yadda ku ga ya rubuta. Inda ya bayyana cewa a 2019 zai zabi Atiku Abubakar ne, Yayinda Gwamna zai zabi zabin Gwamna Yari.

Hakan na nufin mai girma Gwamna bai tare da shugaba Buhari. HUJJA a nan ita ce, Wallahi tallahi da Shehi na yin shugaba Buhari ko miliyan daya za ka baiwa Limanchi ba zai rubuta zai yi Atiku 2019 ba.


Ga irinsu limanchi ta Fara bayyana karara, Amma duk wani jami'in gwamnatin Shehi ba daya da na san yana hidimtawa Dan cin zaben shugaba Buhari a 2019. Haka zalika duk wani da ya dauko Kungiyar da ke tallar shugaba Buhari, to ba zai samu karbuwa ga Gwamnatin jahar Zamfara ba. (Duk Masoya Buhari na gaskiya sun san da haka)


Sai dai abunda har yanzu mu ke akansa shi ne, shugaba Buhari zai ci zaben jahar Zamfara, ko da Shehi bai so insha Allahu.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.

23-1-2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here