Jahar Zamfara, jaha ce da tun Tarihin takarkarun shugaba Muhammadu Buhari tun shekarar 2003 ya ke samun gagaruwamar tarbo daga Talakawan jahar a duk lokacin da shigo jahar, saboda kauna da Fata nagari da talakawan su ke yi masa ne, ya sa bai taba faduwa Zabe a jahar ba. Hatta lokacin da jahar ba hannun jam'iyar da ya yi takara take ba, kamar a 2011 lokacin da Gwamna Mai ci a lokacin yana a jam'iyar PDP shi kuma shugaba Buhari ya yi takara a rosasshiyar jam'iyar CPC.
Kuru'un da Shugaban ya samu a 2015 lokacin da ya lashe zaben da ya kafa Tarihin doke jam'iyar PDP tare da kayar da shugaba mai ci a lokacin (Goodluck Jonathan) ba kananan Kuru'u ba ne al'ummar jahar Zamfara, suka zuba masa. Haka ya tabbatar da zamfara Cikakkun Masoya shugaba Buhari ne.
Sai dai kash! Bayan mun yi nasara zama daga wadanda suka zabi gwamnatinsa, da kyakkyawan fatan zai taka muhimmiyar rawa wajen kawar da matsalar tsaron da ke addabar arewa musamman ma al'ummar arewa maso Gabas. Da burbushin Wanda ke shafuwar jahar Zamfara. Dama lungu da sako na kasarmu najeriya.
Alhamdulillahi Shugaban ya taka rawa, kwarai da gaske a yankin arewa maso Gabas, Inda ta'adin Kungiyar Boko Haram ya karanta a yanzu matukar gaske. Har ana iya bugun gaban anyi nasara ko Kare lagon Kungiyar ta'addanci ta Boko Haram. Yayinda yanzu suka koma harin sari ka noke wanda ke nuna raunin Kungiyar karara....
Sai dai kash! A jahar Zamfara, ba haka abun ya ke ba. Domin ba a taba lokacin da aka dauki rayukkan al'ummar jahar zamfara aka salwantar, aka mayar da dama daga cikin 'ya'yan jahar Zamfara marayu, mataye suka zama gwaggwaren dole, masu arziki suka zama matsiyata, garuruwa suka zama kufai. Kamar lokacin Jagorancin Shugaba Buhari ba.
Duk da cewa mafiya yawan mu talakawan jahar na Dora kacokan Kashi tamanin cikin Dari na matsalar ga Gwamnanmu na yanzu, Wanda shi ne ya yi sakaci da matsalar tun tana karamarta, ta gawurta zuwa Inda take yanzu. Sai dai akwai wasu da dama Talakawan jahar da ke ganin Wallahi akwai sakaci matukar gaske na shugaban Buhari, Wanda shi ne mafi rinjayen nauyi ya rataya na kariyar rayukka da dukiyoyin al'umma ya rataya a wuyansa, ko ba komi shi ne dukkanin rundunonin tsaron kasa ke karkashinsa. Wanda Hakan ya sa suka dawo daga rakkiyar Shugaban.
Abu na biyu shi ne; halin da jam'iyar APC ta jahar Zamfara ke ciki Wanda kowane bangaren na 'yan siyasar jahar ba wai Apcn kurrum ba, su ke cikin zaman zullumi tare da rashin sanin abunda zai faru, Wanda Hakan ya sa harkokin siyasa suka yi tsit! duk da kasa da wata daya suka yi saura babban zaben 2019. Wanda ko shi Gwamnan cikin halin tsaka mai wuya, ya ke. Duk da shi ya canye zanguna biyu da kundin tsarin mulkin kasa ya ba shi damar yi...
Idan mu ka dubi mafiya yawan makaraban shugaba Buhari a Zamfara, da ake tunanen za su iya nema masa Al'umma. ba su da wani amfani ga Al'umma, da har za su iya Tara masa al'umma.
Idan muka Fara da Ministan tsaro Mansur Dan Ali Wanda Dan Asalin Birnin Magaji ne, ba wani tagwammashi ke gare shi ga Al'umma ba. Hasalima ba ni tunanen zai iya Tarawa shugaba mutun dubu uku.
Ba Maganar Jakadu biyu da mu ke da su ake yi ba. Ambasada MAIRIGA da Takwaransa Barista Garba Gajam, ake yi ba. Domin an dai Nada su wannan mukamai ne, dan kurrum su tallafi iyalansu. Kamar yadda zahirin Hakan ya nuna la'akkari da halin suman da suka yi ba wani labarin su da talakan jahar Zamfara ke ji, balantana ya yi tunanen samun sa'ida daga gare su, har talakawan su kaunaci shugaba Muhammadu Buhari Dan su. Dan haka ba mu tunanen za su taka wata rawa wajen shigowar Buhari a Zamfara.
Sai dai ko mene tsantsan son Buhari na nan ga mafiya yawan talakawan jahar, sai dai ya kamata a yi Sara tare da duban bakin gatarin.
Allah ya tallafi kasarmu da jaharmu ta Zamfara ya Dora mu akan tafarki nagari, tare yi Muna Mafita akan kangin rashin tsaron da mu ke ciki, Allah ka baiwa Jagororinmu ikon yi Muna adalci, mu kuma Allah ka ba mu ikon yi masu biyayya da ba ta kaucewa addininka ba.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
22-1-2019

