Yau Assabar 2-2-2019, ne aka rantsar da shuwagabannin Kungiyar dalibbai ta jahar Zamfara. Bikin rantsuwar Wanda ya gudana da dakin taro na JB YAKUB da ke garin Gusau.
Ya samu halartar muhimman mutane, wadanda su ka hada da 'yan siyasa, Ma'aikatan Gwamnati, shugabannin Dalibbai daga ciki da wajen Manyan makarantannin jahar Zamfara.
Barister Bashar Muhammad Maradun. Ya rantsar da dukkanin shugabannin Kungiyar farawa da Shugaban Kungiyar. Da ya ke jawabi a wajen taron. Tsohon Shugaban Kungiyar dalibbai ta jahar Comrade Mubarak Garba. Ya godewa Allah da ya ba shi damar Jagorantar Kungiyar na tsawon Shekara daya, tare da jero tarin nasarorin da su ka samu a lokacin Jagorancinsa. Inda ya roki Allah ya baiwa sabbin Jagororin ikon sauke nauyin da Aka Dora masu.
Da ya ke jawabi a wajen bikin rantsuwar, rantsattsen Shugaban Kungiyar kwamrad Ramadan Mijinyawa, ya bayyana cewa, zai yi Aiki wurjanjan domin daga martabar dalibban jahar Zamfara, ganin yadda ta tabarbare. Daga karshe Shugaban ya roki Allah ba sabbin Shugabannin ikon sauke nauyin da aka Dora masu.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau Zamfara (Mukaddashin Jami'in Hulda da Jama'a Na Kungiyar Dalibbai Ta Jahar Zamfara)
Post Top Ad
Responsive Ads Here
Saturday, 2 February 2019
Home
Unlabelled
AN RANTSAR DA SHUWAGABANNIN KUNGIYAR DALIBBAI TA JAHAR ZAMFARA, YAU!
AN RANTSAR DA SHUWAGABANNIN KUNGIYAR DALIBBAI TA JAHAR ZAMFARA, YAU!
Post Bottom Ad
Responsive Ads Here
Author Details
Templatesyard is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates which are professionally designed and perfectlly seo optimized to deliver best result for your blog.



