Shekaru da dama da suka wuce, dalibbai da Kungiyar dalibbai a jahar Zamfara sun zama cikin halin suma Wanda Hakan ne ya sa kwata-kwata, dalibban jahar Zamfara su ka zama koma baya, in ka kwatanta su da takwarorinsu na wasu jahohin.
Hakan ya sa mu sabbin Jagororin Kungiyar, mu dauki hanyar kawo gyara, domin dalibban jahar Zamfara su yunkuro da karsashinsu a jahar Zamfara.
Ganin cewa yanzu muna a cikin sha'ani na siyasa da yau dudu saura kwanaki goma sha uku a yi zaben shugaban kasa da na 'yan majalissun tarayya, kasa ga mako daya na 'yan Majalisar jaha da na Gwamnoni. Hakan ya sa kungiya ta ga ya dace ta yi kokarin ganin cewa ta yiwa tsarin tafiyar ta ginshikin da zai yi wuyar wargazawa. Ta hanyar biyar daya-bayan-dayan 'yan takarkarinmu. Domin jin irin tanadin da su ka yiwa dalibbai in sun Kai kan karagar mulki.
Wanda da farko dai za mu yadawa duniya, duk abunda mu ka tattauna da su, ko in ce duk alkawarin da su ka yi na tallafawa dalibban jahar Zamfara. Wanda da anci Zabe, za mu nemi su cikawa dalibbai alkawarin da su ka yi masu, kamar yadda mu ka Sanar da duniya kuma muka aje shi a matsayin hujja.
Dan haka daga gobe Talata 5-2-2019 za mu Fara Kai takardun neman zama da duk 'yan takarar da dama ta samu, kuma in Allah ya nufa duk alkawarin da su ka daukarwa dalibbai za mu Sanar da sauran dalibban jahar Zamfara. Wanda Hakan zai taimakawa dalibban ta hanyar sanin kudurorin 'yan siyasar ga dalibban, haka zalika Hakan zai sa su dalibban su San Dan siyasar da ya dace su zaba a zaben 2019 in Allah ya Kai mu.
Allah ya taimaki dalibban jahar Zamfara da Kungiyar baki daya.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau. (Mukaddashin Jami'in Hulda Da Jama'a Na Kungiyar Dalibbai Ta Jahar Zamfara)
4-2-2019
Post Top Ad
Responsive Ads Here
Monday, 4 February 2019
Home
Unlabelled
KUNGIYAR DALIBBAI TA JAHAR ZAMFARA, ZA TA FARA ZIYARAR 'YAN TAKARKARIN ZAMFARA!
KUNGIYAR DALIBBAI TA JAHAR ZAMFARA, ZA TA FARA ZIYARAR 'YAN TAKARKARIN ZAMFARA!
Post Bottom Ad
Responsive Ads Here
Author Details
Templatesyard is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates which are professionally designed and perfectlly seo optimized to deliver best result for your blog.

