jami'an hukumar Hana wadaka da cin hanci da rashawa, (EFCC), Yankin Sokoto, a yau Talata 28, 5- 2019 an Kama Dan siyasar ne dauke da naira Miliyan sittin N60, 000, 000 (Sixty Million Naira) kudi kasa. Wannan ya biyo Bayan rahoton da aka samu sirri da aka samu.
Wanda ake zargin Murtala Muhammad Wanda dan uwa ne ga Sakataren Gwamnatin jahar Zamfara Professor Abdullahi Shinkafi, An Kama shi ne a gida mai Lamba145 Igala Hausing Estate, Off Byepass Road, Gusau, Zamfara State.
Kayan da aka Kama shi da su sun hada da: Toyota Land Cruiser Prado Jeep Baka mai Lamba DKA 67 PX Kaduna tare jikkuna hudu Ghana Must go shake da kudaden kowace dauke da Miliyan sha biyar biyar. Tare bindiga daya (One single barrel gun); tare wata bindiga kirar gida daya (One locally made) da karamar bindiga (Revolve Pistol) da albarussai
Da za an kammala bincike za a tura shi kotu


