YIWA GWAMNATIN MATAWALLE ADDU'A DA FATAN ALHERI, WAJIBI NE GA DUK BAZAMFAREN KIRKI. - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Thursday, 30 May 2019

YIWA GWAMNATIN MATAWALLE ADDU'A DA FATAN ALHERI, WAJIBI NE GA DUK BAZAMFAREN KIRKI.


Tun Bayan da aka kirki jahar Zamfara a 1996 dama dawowar mulkin dimokaradiya a Nijeriya 1999 ba a taba, lokacin da Allah ya nuna tsantsar ikonsa da buwayarsa a fili ga al'ummar jahar Zamfara, kamar a wannan Karon ba. Kuma wannan ya biyo Bayan nuna tsantsar nuna mika wuyan da al'ummar jahar Zamfara su ka yi zuwa gare shi.



Domin na tabbatar ba wanda zai bugi kirjin cewa shi ne ya Kai sabuwar Gwamnatin ko ita ta ce ita ta ce ta kai kanta, kan karagar mulkin Zamfara. Sai dai mu ce Allah nan da mu ka Dade Muna rokon ya yi muna afuwa ya kawo Muna karshen mulkin danniya da aka Shekara da Shekaru ana yi Muna yanzu Allah ta'alla ya karbi addu'rmu. Ya kawar muna da Gwamnatin da duk wani na ta.



Saura da me da farko dole mu ta shi tsaye mu kawar da bambancin da ke tsakaninmu musamman na jam'iya mu rungumi juna mu sanya kishin jaharmu a gaba. Haka zalika dole mu Tashi tsaye wajen marawa wannan Gwamnatin ta kowace fuska tare da kokarin dagewa da addu'o'in samun nasarar Gwamnatin, kamar yadda mu ka yi na roshewar Gwamnatin da ta shude, Wanda da ikon Allah mu ka yi haka za a wayi gari mu yi bankwana da  tarin matsalolin da mu ke fuska.


Dole mu natsu mu yi tuna cewa, ba Bello Muhammad Matawalle ne, zai ci nasara ba in har jahar Zamfara ta ci gaba. Ba mu da wata jaha da ta kai Zamfara, in ta ci gaba ni da Kai za mu karu, in ta ci baya ni dai Kai da kowa zai cigaba.

Domin haka mu rike addu'a da yiwa Gwamnatin fatan alheri, domin addu'ar ce za ta zama jagora a wannan Gwamnati.



Daga karshe ina rokon Allah ya kawar da girman Kai da rashin jin shawarar da ta yi tasiri ga tsohowar Gwamnati, Allah muna rokonka, ka rika ma wannan Gwamnatin ka ba ta ikon yi Muna adalci, Allah ka ba ta ikon sauke hakkokinmu da su ka rataya a wuyanta. Allahumma amin.


Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau

25-9-1440
30-5-2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here