SENATOR MARAFA ZAI FARANTA RAN TALAKAWA A WATAN RAMADAN! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Sunday, 5 May 2019

SENATOR MARAFA ZAI FARANTA RAN TALAKAWA A WATAN RAMADAN!




Sen. Kabir Garba Marafa con. Ya bada umurni a fara raba buhu dubu (1000) Na Masara  hadi da shinkafa 300 ga Magoya bayansa wayanda Allah ya ciyar domin fara hidimar azumi dake gabanmu,

Wanda Tuni jagoran Tafiyar Alh. Surajo Garba Mai katako  ya fara aiwatar da umurnin sanata Marafa wajen mika wannan alheri ga Mutanen da Allah ya ciyar acikin wannan abinci,

Hali ne na tausayi wanda ya saba tausayawa al'umma zaiyi wahala ya kasa,

Sen. Marafa ya zama abun koyi ga yan siyasar kirki masu son tausayawa al'umma yakan bude hanya ga takwarorinsa hanya mafi inganci ta mayar da alheri ga alheri acikin al'ummarsa,

Wakili ne wanda yayyi amfani da damar da Allah ya bashi ta wakilci wajen yin ayyukkan alheri acikin al'umma da kuma yankin da yake wakilta,

Wannan yassa yake samun tagomashi tare da gudunmuwar addu'oin  al'umma,

Muna rokon Allah ya kara mashi jagora kuma ya tsaya mashi inda baya iya tsayawa kansa, Allah ya zama gatansa da dukkan mabiyansa da masu mashi fatar alheri,

Amin.

Shamsu Kasida
05/05/2019.

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here