Tun dawowar mulkin dimokaradiya a Nijeriya da ma kirkirar jahar Zamfara a 1996 jam'iyar PDP ba ta taba cin Zabe a jahar Zamfara ba. Duk da a 2007 Gwamnan da ke ci a Zamfara ya koma PDP Inda ya fadi Zabe a 2011.
Idan mu ka dubi dalillan da su ka sa PDP ta fadi Zabe a 2011 a Zamfara da 2019 da ta fadi na duk yan Majalisar tarayya da na wakilai (dama dai na Shugaban kasa ba tsammanin za su Kai banten nasu su ke yi ba)
Za mu ga cewa tsantsar rashin tanadi da daukar siyasar ba da gaske ba ne ya Kai ga haka Hasalima da dama suna siyasar ne Dan kasuwanci ba Dan su ci zabe ba. Mafi yawansu. Domin Idan mu ka dubi halin da talakawan jahar Zamfara su ke ciki, na neman canji ruwa a jallo da kuma irin matsalolin da jam'iyar APC ta yi ta fuskanta Wanda har kasa da awanni 50 a yi Zabe jam'iyar ba ta da tabbacin shiga Zabe. Wanda Hakan ya taimaka matukar gaske na rashin yin kyakkyawan tanadi da 'yan takarar APC ba su yi ba.
Da kuma irin yadda har aka kammala Zabe Hasalima wasu daga cikin masu Zabe din ba su da tabbacin wadanda su ka zaba a APCn.
Wanda na tabbatar wannan damar da kuka samu da tun farko kun shirya kwatar goruba a hannun kuturu, da Tuni kun kwace ta. Ko da ko wani bangare ne na goribar. Sai dai! Kash! Ba wani tasiri da jam'iyar ta yi in banda zama yar rakkiya kamar yadda ta Saba zama a Zamfara.
Hujja a nan ita ce;
Idan mu ka dubi tun tashin farko yadda 'ya'yan jam'iyar ko in ce Jagororinsu su ka yi kunnen uwar shegu, a matsayinsu na jam'iyar adawa, aka yiwa Zamfarawa yadda aka so, ba wani kul! Da jam'iyar ko Jagororinta ke cewa, Wanda Hakan ya sa da dama mu talakawa mu ce duk kanwar ja ce tsakaninku da APC mai mulkin!
Haka zalika Idan mu ka dubi yadda Jagororin jam'iyar su ka yi kwancinsu, ba tare da sun nemi mutane ba, ko fitar da kyawawan manufofinsu a fili ba. Wanda Hakan ya haifar da rashin sanin su waye ma a PDPn. Misali akwai tarukka uku na bayyana kudurorin 'yan takarar Gwamna da aka yi a jahar Zamfara. Ba daya da aka samu Dan takarar Gwamna a jam'iyar PDP ya halarta, assalima daya ne daga cikinsu aka samu ya tura Dan takarar Sanata Mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya, Wanda sauran Dayan bai tura kowa baya daya kuma wani mutun ne daban akan tura, Wanda shi ne ya tsaya a madadin Dan takarar Gwamna a PDPn shi ne ya yi wa al'ummar Zamfara alkawulla tare da amsa tambayoyin Zamfarawa. Wanda tun daga lokacin mu ka Fara gano an Fara Saka da bakin zare!
Da kuma yadda aka kawo yan takarkari da kwata-kwata ba wani tagwammashi su ke da shi cikin al'umma ba. In ka debe matashi daya mai takarar wakilcin Gusau da Tsafe a Majalissar tarayya Hon. Kabiru Amadu. Babu wani Dan siyasa a Zamfara baki daya da ya tallata PDP da kudurorinta. Sai dama-dama a yankin zamfara ta Arewa Inda tsohon Sanata Sahabi Ya'u ya yi takarar Sanata. Wanda duk da har wadannan yankunan PDP ta fadi Amma dai ta taka rawa a nan, sai dai rashin kishi jam'iyar da ma al'umma ya sa kwata-kwata jam'iyar ta samu matsala a can. Wannan kenan.
Haka zalika Idan mu ka dubi yadda ita PDP ta rika tarbon mutane, tun kafin ranar zabe, dama lokacin zaben za mu ga cewa sun takawa Kansu mummunar rawa wajen kasa cin ko da karamar hukumar mulki daya uwa uba kananan hukumomi biyu da zai kai sun samu Dan Majalissar tarayya.
Misali ni nan ni ne Mukaddashin jami'in Hulda Da Jama'a na Kungiyar dalibbai ta jahar Zamfara baki daya. Mun bukaci ganawa da dukkanin 'yan takarar Gwamna a Zamfara har zuwa yan Majalisar tarayya. Wanda alhamdulillahi mun zauna da dama daga cikin 'yan takarar na wasu jam'iyu. Amma abun mamaki, in ka debe Hon. Kabiru Amadu, ba mutun daya a PDP da ya ba mu damar zama da shi, duk da ba daya daga cikinsu da ke kan karagar mulki (balantana su ce mutane sun yi masu yawa). Kuma ba daya daga cikin mafi yawansu da ba mu yi yunkurin baiwa takardar neman zaman ba. Wai fa a cewarsu mutane sun yi masu yawa.
Wanda ina ganin ko yanzu ranar 9-3-2019 da za a yi zaben Gwamna PDP ba za ta iya cin Zabe a jahar Zamfara ko da a mazaba daya tilo! Ba wai dan Al'umma na kaunar APCn ne a cikin zuciyoyinsu ne ko suna jin dadin Jagorancinta da aminta da manufofin 'yan takarar ba. A'a sai dai dan rashin sanin Wanda zai Mara masu da Kara masu karfin guiwar in sun zabi ra'ayinsu zai kai ga Tudun mun tsira
Dan haka shawara ta rage wa mai shiga rijiya. In ya so zai iya shiga ta ka, ko da kafa!
Amma dai al'ummar jahar Zamfara ya kamata mu Kara yiwa kanmu karatun ta natsu, mu natsu tun tashin farko mu Kalli Al'umma masu tagwammashi mu bi su ba wai jam'iyar da su ke Kai ba. Haka zalika mu yi kokarin Kallo dukkanin Jagororinmu su waye su, me sunka yi Muna a LOKACIN yakin neman Zabe. Kuma mi za su yi Bayan sun ci zaben!
Allah muna rokonka, Jagororin da ka nufi za su Jagorance mu, ka ba su ikon kwatanta Muna adalci, Allah ka rika masu kada ka bar su da iyawarsu. Allah duk wani mugun hali nasu ka shafe shi zuwa nagari. Allah ka ba su ikon sauke nauyin da mu ka Dora masu
Allah ka ganin matsalar jahar Zamfara, Kai dai ke iya maganinta. Allah ka yi Muna maganinta, ka damka mu hannun Gwamna adili da 'yan majalissu na jaha jajirtattu kuma adilai. Allahumma amin.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
27-2-2019
Post Top Ad
Responsive Ads Here
Wednesday, 27 February 2019
Home
Unlabelled
JAM'IYAR PDP KU KUKA KAYAR DA KANKU A ZAMFARA, KUMA, ZA KU FADI A ZABEN GWAMNA DA KE TAFE !
JAM'IYAR PDP KU KUKA KAYAR DA KANKU A ZAMFARA, KUMA, ZA KU FADI A ZABEN GWAMNA DA KE TAFE !
Post Bottom Ad
Responsive Ads Here
Author Details
Templatesyard is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates which are professionally designed and perfectlly seo optimized to deliver best result for your blog.

