KIRA GA HUKUMAR ZABE DA JAMI'AN TSARON KASARMU: YA KAMATA A SAUYA RANAR ZABE A JAHAR ZAMFARA! - MAIBIREDI TV

MAIBIREDI TV

Na kirkiri wannan blog ne, domin kawo labarai na ciki da wajen Najeriya dama rubutu akan ababen da ke faruwa a jahar Zamfara.

Breaking

Home Top Ad

Responsive Ads Here

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Tuesday, 19 February 2019

KIRA GA HUKUMAR ZABE DA JAMI'AN TSARON KASARMU: YA KAMATA A SAUYA RANAR ZABE A JAHAR ZAMFARA!


Jahar Zamfara jaha ce da a baya babu wata jaha da ta kai jahar zaman lafiya sai dai kash! Yanzu babu wata jaha da al'ummarta  ke cikin tashin hankali kamar Zamfara. Kullum cikin tashin hankali mu ke ana kisanmu kullum, ana satar mutane ana yi Muna kisan kiyashi dukiyarmu ana kone ta ba gaira ba Dalili. Mataye da dama sun zama zawarawa, 'ya'ya da dama sun zama marayu, masu kudi da dama sun koma matsiyata sun koma Baran abunda za su ciyar da Kansu da iyalansu.

Ba damar shiga da ficen kirki a jahar Zamfara. An koma kullum cikin satar mutane ake har a cikin manyan garuruwan zamfara, Bayan yiwa kauyukka Kat!

La'akkari da halin da mu ke ciki. Da kuma yar manuniyar da ta faru a MAKON da ya shude. Inda aka Kama mota dauke da bindigogi a Gusau, dama kuma yadda aka ta samu labarin rashin tsaro Wanda har sace wasu daga cikin ma'aikatan zaben da su ka tafi da sunan yin aikin a karamar hukumar mulkin Tsafe aka yi. Wanda yanzu haka mutanen na hannun masu garkuwa da mutane. Wanda Hakan ya sa mafi yawanmu da za mu yi aikin zaben guwayun da damanmu su ka Sanyi ga aikin Zaben. Har mun debe rai da komawa wajen aikin a makon gobe, Dan kariyar rayukkanmu.

Dan haka Muna amfani da wannan damar, mu yi Kira ga ita hukumar zabe, dama jami'an tsaron kasarmu, da su dubi yuyuwar sauyawa al'ummar jahar Zamfara ranar zabensu.

La'akkari da halin da jahar ta ke ciki, da kuma karancin jami'an tsaron da jahar da ma kasar ta ke fuskanta. Wanda Wallahi jami'an tsaron da ke jahar Zamfara da ma wadanda aka kawo da sunan Zabe, ba za su iya baiwa jahar tsaron da ya da dace har a yi zaben nan kamar yadda aka saba ba. Wanda ko da za su iya, to bakin tsoron da ya cika Muna zuciyoyi na hudawar da aka yi makon da ya wuce, ba zai bar da dama daga cikinmu zuwa zuwa wajen da aka tura mu aikin zaben ba. Hakan na nufin za a samu karancin ma'aikata kwarai da gaske.

Dan haka kamata ya yi ita jahar Zamfara a canza mata ranar zabenta, a mayar da ita ko da ranar Aiki ne, Wanda Hakan zai taimaka, a kawo Karin jami'an tsaro daga makwabtan jahohi, Wadanda za su isa a tura su lungu da sako na jahar Zamfara.

Daga karshe Muna rokon Allah ya sa Kokenmu ya Kai ga kunnuwan da mu ka yi koken Dan su, ya kuma ba su ikon share Muna hawayenmu.

Allah ka zaunar da Zamfara da Nijeriya lafiya. Allah ka sa a yi wannan zaben lafiya a kammala lafiya, Allah ka baiwa jami'an tsaronmu ikon murkushe duk wani Dan ta'adda da ke gurin gurgunta zaman lafiya a jahar Zamfara da Nijeriya baki daya. Allah ka zaba muna shuwagabanni addilai.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau Zamfara.

19-2-2019

Post Bottom Ad

Responsive Ads Here